lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Ubangiji ya gwabunta ladanmu da naku da tunawa da ranar shahadar kofar biyan bukatu Imam Musa Alkazim (as).


Lallai ba kowa bane mai wannan manya manyan kakanni da ya zarce Imam Musa Alkazim (as) ibn Jafar Sadik ibn Muhammad Albakir ibn Ali Zainul Abidin ibn Sayyidul shuhada’u Husaini ibn Ali ibn Abi dAlib (as).

Mahaifiayarsa: Hamida barbariyya diyar Sa’id anemata lakabi da (Musaffatu) an rawaito cewa asalinta daga kasar Andalus ne ana kuma kiranta da (lu’lu’atu) baiwa mai daraja wadda Imam bakir ya saye ta ya kuma yi kyautar ta ga `dansa Imam Sadik ... cigaba

Adalci hadafin daukacin addinai

Da sunansa madaukaki
Tsira da aminci su tabbata ga annabin rahama da iyalansa tsarkaka
Hakika adalci shi ne himmar dukkanin mutumin kirki a tsawon tarihi, a kowanne zamani baka rasa masu ji da ganin larurar samar da adalci wanda shi ne burin dukkanin mutane tun farkon duniya har zuwa wannan zamani namu, kamar yanda masu zurfin tunani cikin mutane da masana falsafa da hikima sun yi bincike cikin wannan batu da ya bayyana himmatuwarsu.
... cigaba

Amsar SAYYID Adil ga D.R Kubaisi



Da sunan Allah mai rahama mai jin kai



dana na kaina mai neman sanin gaskiya da hakikanin al’amari hakika abin da mai ambaton tarihi ya Ambata kadai ba wani abu bane face jinkirtaccen al’amari daga tarihi wanda malaman tarihi yaran sarakuna da yan kanzagin halifofi da sarakuna daga Umayyawa da Abbasiyawa kamar yadda dama a dabi’ance yake cewa za su rubuta abubuwan da sarakuna da halifofin zalunci da danniya suke so, musammam ma da yake ma akwai yunkurinsu na wanke zalincin da sukai da barnarsu da danniya kan al’ummu da imani da muslunci, saboda haka ba zai yiwu a iya dogaro da tarihin da alkalaman da aka dauke haya aka biya su kudi suka rubuta ba da ya kasance ... cigaba

Ayoyin samun nutsuwa

wadanne ayoyi ne ayoyin samun nutsuwa meye ye falalarsu? ... cigaba

dangantakar addini da siyasa

Cikin wannan darasi:
1- akwai tabbatar damfaruwar addini da siyasa cikin ba'arinsu da ba'ari da kallon zuwa ga mahiyyar addini da tsarin yadda annabawa suka rayu da ma'asumai amincin Allah ya kara tabbata a gare su da kuma ayoyin kur'ani mai girma.
... cigaba

Falsafa da siyasa cikin muslunci

Falsafa da siyasa cikin muslunci ... cigaba

GISHIRI CIKIN TAFIN HANNU



An hakaito cewa a wata rana wani yaro matashi ya ji rashin gamsuwa da yanda rayuwarsa take gudana da dukkanin abin da yake kewaye da shi ... cigaba

GUDUMMAWAR IMAM SADIK (AS) YA BAYAR DON GINA AL’UMMA



Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Gabatarwa

Hukumar Umayyawa ta yi rusau mai fadin gaske cikin ginin zamantakewar al’ummar musulmi ta kasance tana rainon kungiyoyin bata da karkacewa daga kan hanyar gaskiya wanda suke harin kwakwalen musulmai da fahimtarsu suka zama silar haifar da bakuwar sakafa cikin musuluci, daga baya kuma sai hukumar Abbasiyawa ta dare karagar mulki domin ita ma ta kammala wannan rusau da umayyawa suka fara, sau da yawa da wasu sabbin uslubai, babban abin da ke gaban hakan ma shi ne rushewar zamantakewa da karkatar tunani da na suluki mai girma, Imam Sadik (as) ya kasance yana da babbar rawar da ya taka cikin yakar wannan barna ta hanyar assasa makarantun ilimi da samar da alakokin zamantakewa domin sake karfa ginin muslunci da zamantakewar da ya karbo daga babansa da kakanninsa tsarkaka. ... cigaba

Hasken sasanni cikin sanin arzuka

Allah mai yawan azurtawa ne kuma shi ma’abocin karfaffen karfin ne ya umarce mu daga ludufin sa da mu roke shi mu nema daga gare shi, abin ban mamaki daga hakan shi ne cewa shi ubangiji bai damuwa da bawa ba don addu’ar da yake yi ba da nema daga gare shi, hakan yana kasantuwa daga mukamin bauta da kaskantar da kai ta yiwu ma cikin mukamin shagwaba ... cigaba

Imam Sadik (as)


Hasken rana ilimi da malamai
Tunda aka haifi Imam Sadik (as) hasken tunaninsa yake haskaka kalamansa suke yaduwa da jawo hankula ta yanda zukata suka karkato zuw aga soyayyarsa daga kowanne da kwari, Imam Sadik ya kasance alkiblar gama garin mutane da malumma shi iliminsa babban tafki ne ta yanda malamai basu iya kamfata daga gareshi face cikin cokali saboda tsananin yalwarsa mara iyaka. ... cigaba

Tura tambaya