sababun makaloli
- fikihu » KARIJUL FIKHU 27 RABIU AWWAL 1441 H CIKIN TA'ARIFIN IJTIHADI A ISDILAHIN FIKHU TSAKANIN SUNNA DA SHI'A
- fikihu » KARIJUL FIKHU 5 GA WATAN RABI’U AWWAL SHEKARA 1441
- muhadara » GISHIRI CIKIN TAFIN HANNU
- muhadara » Malamai magada Annabawa_ kashi na 3 tarihin Shaik Abbas Qummi
- hadisi » Muhimman wasiyoyi uku daga Imam Sadik (as)
- fikihu » Bahasul karakul fikhu: fatawa halascin karanta surori biyu
- hadisi » KASHE KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALAYEN SU
- hadisi » Ashabul Ijma da siffofin hadisi
- hadisi » Sirri daga sirrikan Sayyada Fatima Ma’asuma (a.s)
- muhadara » Rigima da dauki ba dadi tsakanin hankali da wahami
- muhadara » kada ku kauracewa wannan kur'ani
- hadisi » Addu’a mabudin ibada
- muhadara » Mace da tawayarta
- muhadara » Nasiha ga masu shirin yin aure
- muhadara » Adalci hadafin daukacin addinai
makaloli
- fikihu » shin riwayoyin da suke cewa salmanu Farisi da Abu zar lokacin dawowar imam zaman (as) suna daga cikin matamaimakansa riwayoyi ne ingantattu
- fikihu » Ta ƙaƙa za mu iya karɓa ko dogaro da masdarin hadisi tareda cewa kwafin asalin masdarin wasu ba’arin malamanmu sun karɓe shi ne da kyautata tsammani ba tareda sun san asalin marawaicin hadisin ba ku sun taɓa ganinsa
- muhadara » Siyasar muslunci zama na Arba’in da shida
- fikihu » Hasken haskaye nutsuwar zukata
- fikihu » Bahasul karakul fikhu: fatawa halascin karanta surori biyu
- muhadara » dangantakar addini da siyasa
- muhadara » kada ku kauracewa wannan kur'ani
- fikihu » Shin saukar kur’ani daga tajalli ne ko ko daga nisanta ne?
- muhadara » Rigima da dauki ba dadi tsakanin hankali da wahami
- muhadara » Karanta, yi tunani, ka yi aiki, ka san makiyinka Shaidan
- muhadara » Ubangiji ya gwabunta ladanmu da naku da tunawa da ranar shahadar kofar biyan bukatu Imam Musa Alkazim (as).
- fikihu » Ku tashi tsaye domin Allah
- muhadara » Hasken sasanni cikin sanin arzuka
- muhadara » Ta Yaya dalibi zai iya sanin gobensa
- hadisi » KASHE KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALAYEN SU
Mukalolin da akaranta dayawa.
- fikihu » Sirri daga sirrikan manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata gare shi da iyalansa-tare da alkalamin samahatus sayyid Adil-Alawi (dz)
- muhadara » Ta Yaya dalibi zai iya sanin gobensa
- hadisi » KASHE KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALAYEN SU
- hadisi » Sirri daga sirrikan Sayyada Fatima Ma’asuma (a.s)
- hadisi » Malamai sune magada Annabawa
- fikihu » Ku tashi tsaye domin Allah
- muhadara » KISSAR SOYAYYA
- fikihu » Muna ta’aziyya ga daukacin al’ummar musulmi bisa munasabar tunawa da wafatin sayyada Fatima `yar imam Musa Alkazim (as) wacce akewa alkunya da (ma’asuma) amincin Allah ya kara tabbata gare ta.
- fikihu » Hukunce-hukuncen muslunci
- muhadara » tsari daga sharrin Iblis
- muhadara » Kyawawan halayen likita ne a muslunci
- muhadara » Mace da tawayarta
- muhadara » Ayoyin samun nutsuwa
- fikihu » Sakon ziyarar arba’in cikin iraki-tattaunawa tare da samahatus sayyid Sami badari.
- fikihu » Tambaya a takaice: kasantuwar ya zo cikin hadisi cewa hazrat Fatima (as) a wata rana bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) tayi shaukin ganin Salmanul farisi sannan Fatima lokacin haduwarta da Salmanu ta sanya gajerun kaya, yaya za ai bayani kan wannan hadis
Bahasul karakul fikhu: fatawa halascin karanta surori biyu ko fiye da haka cikin raka’a guda tare da karhanci hakan cikin sallar farilla- zaman a 101 16 ga watan sha’aban
Mas’ala ta 10: fatawa shi ne halascin karanta surori biyu ko fiye da haka cikin raka’a guda tare da karhancin hakan cikin sallar farilla, ihtiyadi barin yin hakan, amma sallar nafila to ita cikinta babu karhancin.
Ina cewa: shin ya halasta a karanta surori biyu cikin raka’a daya wannan shi ne abin da kur’ani yake bayanin sa tare da wasalin kasara da harafin kafun- ko kuma dai bai halasta ba, cikin wannan mas’ala malamai sun samu sabani, wannan mas’ala tana fuskoki:
Ta farko: halascin cudanya surori cikin farilla da rashin halascin hakan, an samu daga mutum fiye da daya daga cikinsu bari dai gungun jama’a masu yawa sun tafi kan halascin hakan kamar yanda yake wurin Akaramakallahu Allama Hulli (ks) hakika ya hakaito shi cikin littafin Kashaful Lisam daga Al’istibasar da Assara’u da Shara’i’I da Almu’utabar da Jami’u da litattfan Shahid, a cikin Kashaful Lisam ya oc cewa hakan shne Magana mafi karfi, an karfo daga Allama Majalisi (ks) cikin Biharul Anwar ya danganta halascin ga jamhur din malamai da suka zo bayan magabatan farko da wanda suka zo bayansu.
Haka ya danganta zuwa ga mafi shahara tsakanin malumman farko kan rashin halasci, bari dai daga Malamin mu Shaik Saduk (ks) cikin Amali: 41:7 cewa hakan daga addinin Imamiyya yake, daga Assayidul Murtada Alamul Huda (ks) ace: hakan yana daga abin da Imamiya suka dayantu da shi (Al’intisar:146)
Sannan daga cikin wanda ya tafi kan halasci ya tafi kan karhanci ma’ana karhanci cudanya tsakanin surori biyu cikin raka’a daya cikin farilla, abin nufi daga karhanci shi ne mafi karancin lada kamar yand ake fada cikin makaruhai cikin ibada kamar yanda kae cewa makaruhi ne yin Sallar cikin bandaki ma’ana ladan sallar yana kasa da yin ta cikin gida ko cikin masallaci, bawai ana nufin ta da ma'anar isdilahin da yake kishiyantar mustahabbi ba da ma’ana rinjayar da barin yin aiki, lallai da ya kasance da wannan ma’ana cikin ibada da ya lazimta bautuwa da abin da aka hana wannan rufaffe ne daga abin da baya halasta lallai ba neman kusancin ubangiji da abin da akai hani kansa babu banbanci cikin kasantuwar sa daga haramun ko karhanci, abin nufi daga wannan karhanci cikin ayyukan ibada shi ne lada mafi karanci.
Bai buy aba cewa tushe da mabubbugar sabani tsakankanin manyan Malamai galibi kadai dai yana kasancewa ne daga fuskar harshen riwayoyi da kasantuwar kowanne ayari daga riwayoyin suna karbar cin karo da juna da kuma faduwa sakamakon kafadantuwar su da kuma komawa zuwa ga asalul Amali.
Cikin wannan mukami akwai wanda ya tafi kan haramcin cudanyawa kamar yanda ya kasance wajen malumman farko har ya zuwa zamanin wanda suka Makara suka zo bayan su ma’ana ya zuwa zamani Shaik Mufid da Shaik Dusi (ks) ya zuwa zamani Allama Hulli da Muhakkikul Hulli kadai dai yana riko da ayarin farko daga riwayoyin da suke ingantattu da suke hani, daga cikin su akwai:
صحيحة محمد بن مسلم عن أحدهما عليهما السلام قال: سألته عن الرجل يقرأ السورتين في الركعة، فقال: لا، لكل سورة ركعة ([1]).
Ingantacciyar Muhammad bn Muslim daga dayan su (as) ya ce: na tambaye shi dangane da mutumin d ayake karanta surori biyu cikin raka’a daya, sai ya ce: a'a hakan bai inganta, sai dai cewa ya karanta sura guda daya.
Fuskar kafa dalili: da farko buyan sunan Imamin da aka danganta riwayar zuwa gareshi bai cutar wa sakamakon girmamar Muhammad bn Muslim lallai shi kadia yana nakaltowa ne daga Ma’asumi (as) kamar yanda aka fadi hakan cikin riwayoyin zurara.
Ta biyu: isnadin riwayar ingantacce ne babu wata kura da matsala cikin sa, na uku abin da take shirywarwa zuwa gareshi bayyane yake bata kasa ta gaza ba, hakika hani yayin idlakin sa yana shiryarwa zuwa ga haramci kamar yanda fi’ili amri yake fa’idantar wajabci sai dai idan wata shaida ta bayyana kan sabanin haka.
ومنها: موثقة عبد الله بن أبي يعفور عن ابي عبد الله عليه السلام قال: لا بأس أن تجمع في النافلة من السور ما شئت ([2]).
Daga cikin su: muwassakatu Abdullah ibn Abu Ya’afur daga Abu Abdullah (as) ya ce: babu laifi ka cudanya surorin da ka so ciki nafila.
Fuskar dalili: bayan ingantar isnadi lallai kore laifin cudanyawa cikin nafila yana shiryarwa kan cewa akwai laifi cikin farilla sakamakon mafhumul wasaf da tafiya kan hujjantakar sa, lallai zahiri al’amari daga kayyadewa cikin rashin lafi a nafila lallai salla ba tare da idlaki ko kaidi ba tana tattaro farilla da nafila wanda yake nuna bata kasance muhallin cudanyawa ba, bari dabi’a kayyadadda (ma’ana sallah tare da sanya kaidin farilla ko nafila) itace muhallin halasci ko rashin sa, wanda ta kasance sallar nafila a kebance, ba da ban hakan ba a wannan lokaci da ya lazimta lagawiyya rashin ma'ana da fa'idar kaidi da kayyaduwa, daga cikin tabbatar da halasci da rashin laifi cikin nafila zamu gane cewa bai halasta ba cikin farilla kaga abin da muke nema ya tabbatu Kenan.
ومنها: رواية منصور بن حازم: محمد بن يعقوب: وعن أحمد بن إدريس عن أحمد بن محمد بن يحيى عن محمد بن عبد الحميد عن سيف بن عميرة عن منصور بن حازم قال:
قال: أبو عبد الله عليه السلام: لا تقرأ في المكتوبة بأقل من سورة ولا بأكثر ([3]).
Daga cikin su: riwayar Mansur bn Hazim: Muhammad bn Yakubu daga Ahmad bn Idris daga Ahmad bn Muhammad bn Yhaya bn Muhammad bn Abdul Hamid daga Saifu bn Umairatu daga Mansur bn Hazim ya ce: Abu Abdullah (as) ya ce: cikin sallar farilla kada ka karanta kasa da sura guda ko fiye da ita.
Fuskar dalili: amma shiryarwarta babu gazawa ciki lallai hani yana shiryarwa zuwa ga haramci da rashin halasci, saboda haka babu rarrabawa cikin sura daya kamar yanda babu cudanya surori biyu.
Kadai Magana tana cikin isnadi, daga manyan malamai akwai wand ayake ganin isnadin yana da rauni sakamakon kasantuwar Saifu bn Umairatu lallai shi mabiyin mazhabar wakifiyya neya kuma kasance sika, wanda ya tafi kan raunin sa sakamakon abin da ya ginu kai cikin karbar marawaici da ya kasance adali ba shi ne matsaya ba ta kaka mai gurbatacciyar mazhaba zai kasance adali, daga nan ba a karbar hadisin sa kamar yanda wannan shi ne maginar Shahidul Awwal da Shahidus sani cikin Lum’atu da sharhinta kamar yanda ra’ayin su ya kasance kan Sukkuni da Naufali kamar yanda hakan shi ne ra’ayin mai littafin Almadarik da Assayid Amili (ks)
Bayan sai ya tafi kan raunanar isnadin (Almadarik j 3 sh 356) kamar yanda mai littafin Hada’ik ya tafi kai (Alhada’ikul Nadira j 8 sh 46)
ba’arin manyan malamai na wannan zamani sun tafi kan cewa zai yiwu raunin isnadi ya kasance ta fuska lallai Ahmad bn Idris ba zai yiwu ya rawaito daga Ahmad bn Muhammad bn Yahaya ba, sakamakon sabanin daba’a, saboda haka kodai riwayar ta kasance mursala ko kuma an samu kuskure ta hanyar hanyoyin da aka kwafo ta, sai ya bada amsa kan wannan tsammani da cewa yayi rauni da yawa, da cewa ingantacce daga Muhammad bn Ahmad bn Yahaya yake bawai daga Ahmad ba, abin da yake karfafar haka shi ne galibi Muhammad bn Ahmad yana rawaitowa daga Muhammad bn Abdul Hamid.
Sai dai cewa bayan bibiyar kwafin Alkafi da Wasa’il da Attahzib ya bayyana cewa riwayar an nakalto ne daga Muhammad bn Ahmad bawai daga Ahmad ma’ana an nakalto ta daga `dan kuma shi sika ne bawai daga mahaifin sa ba, a wannan lokaci sai ya zamanto ya lazimta faduwar Kalmar (Muhammad) daga kwafin Wasa’il cikin sabon bugun sa hakama Al’istibsar sabon bugu.
Kan wannan ne: da farko: shi Siafu bn Umairatu muwassak ne duk da kasancewa `dan wakifiyya, magina karbar sika cikin nakali ko da kuwa bai kasance adali ba kamar misalin masu gurbatattun mazhabobi.
Na biyu: Muhammad bn Ahmad sika ne da wannan sabanin daba’a yake zama ya kauce, riwayar tana kasancewa mai ingantacce isnadi ba tare da wani ishkali ba, ka lura sosai.
Lallai shi ya kawo ishkali kansa da cewa cikin isnadin akwai Muhammad bn Abdul Hamid wanda manyan malamai sun yi sabanin cikin sikkantan shi ta fuskanin kokwanto cikin komantar da tausikin Najashi ya zuwa mahaifin ko `dan da farko, da kuma rashin kasantruwar Muhammad bn Abdul-Hamid daga shehunan Ibn Kaulawaihi ba tare da wasida ba, ta yiwu raunanar isnadin da mai littafin Almadarik yayi yayi ne yana mai la’akari da wannan al’amari ta wannan fuska.
Wannan sune jimillar daga riwayoyi da suka shirywar kan rashin halasci, sai dai cewa kuma suna cin karo da wani ayarin riwayoyin da suke shiryarwa kan halasci kamar misalin ingantacciyar riwayar Aliyu bn Yakdinu
قال: سألت أبا الحسن عليه السلام عن القرآن بين السورتين فيالمكتوبة والنافلة قال عليه السلام: لا بأس ([4]).
Ya ce: na tambayi Abu Hassan (as) dangane da cudanya tsakanin surori biyu cikin nafila da farilla sai amincin Allah ya kara tabbata a gareshi ya ce babu laifi.
Fuskar dalili: hakika isnadin da abin da take shirywarwa babu wata kura da matsala cikin su.
Hada tsakanin riwayoyin masu karo da juna duk yanda hakan ya yiwu shi yafi dacewa daga watsi da su baki daya, sai a tafi kan hada tsakanin su da ma’anar a dora hanin cikin ayarin farko kan karhanci, abin da ya zo cikin wasu hadisan da suke shiryarwa zuwa ga karhanci yana shiryarwa zuwa gareshi.
Hadisin zai zo nan gaba da yardar Allah ta’ala.