sababun makaloli
- fikihu » KARIJUL FIKHU 27 RABIU AWWAL 1441 H CIKIN TA'ARIFIN IJTIHADI A ISDILAHIN FIKHU TSAKANIN SUNNA DA SHI'A
- fikihu » KARIJUL FIKHU 5 GA WATAN RABI’U AWWAL SHEKARA 1441
- muhadara » GISHIRI CIKIN TAFIN HANNU
- muhadara » Malamai magada Annabawa_ kashi na 3 tarihin Shaik Abbas Qummi
- hadisi » Muhimman wasiyoyi uku daga Imam Sadik (as)
- fikihu » Bahasul karakul fikhu: fatawa halascin karanta surori biyu
- hadisi » KASHE KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALAYEN SU
- hadisi » Ashabul Ijma da siffofin hadisi
- hadisi » Sirri daga sirrikan Sayyada Fatima Ma’asuma (a.s)
- muhadara » Rigima da dauki ba dadi tsakanin hankali da wahami
- muhadara » kada ku kauracewa wannan kur'ani
- hadisi » Addu’a mabudin ibada
- muhadara » Mace da tawayarta
- muhadara » Nasiha ga masu shirin yin aure
- muhadara » Adalci hadafin daukacin addinai
makaloli
- fikihu » KARIJUL FIKHU 27 RABIU AWWAL 1441 H CIKIN TA'ARIFIN IJTIHADI A ISDILAHIN FIKHU TSAKANIN SUNNA DA SHI'A
- muhadara » kada ku kauracewa wannan kur'ani
- muhadara » Imam Sadik (as)
- muhadara » dangantakar addini da siyasa
- muhadara » Falsafa da siyasa cikin muslunci
- fikihu » siffofin jagora
- hadisi » Wajabcin Kiyaye Hadisai2
- muhadara » Nasihar mahaifi ga dansa
- hadisi » Addu’a mabudin ibada
- fikihu » Falalar ilimi da malamai
- hadisi » tauhidi daga hadisai
- fikihu » Ina jin rauni lokutan sallah da addu’a kai kace akwai wani hijabi da shinge da suka katange zuciyata daga riskar debe haso da jin dadi daga garesu
- muhadara » Karanta, yi tunani, ka yi aiki, ka san makiyinka Shaidan
- fikihu » KAN HANYAR SHUGABAN SHAHIDAI IMAM HUSAINI (AS)
- fikihu » Shin imam Ali amincin Allah ya kara tabbata gareshi ya kasance yana yin aiki sannan wanne aiki yake yi?
Mukalolin da akaranta dayawa.
- fikihu » Sirri daga sirrikan manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata gare shi da iyalansa-tare da alkalamin samahatus sayyid Adil-Alawi (dz)
- muhadara » Ta Yaya dalibi zai iya sanin gobensa
- hadisi » KASHE KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALAYEN SU
- hadisi » Sirri daga sirrikan Sayyada Fatima Ma’asuma (a.s)
- hadisi » Malamai sune magada Annabawa
- muhadara » KISSAR SOYAYYA
- fikihu » Ku tashi tsaye domin Allah
- fikihu » Hukunce-hukuncen muslunci
- fikihu » Muna ta’aziyya ga daukacin al’ummar musulmi bisa munasabar tunawa da wafatin sayyada Fatima `yar imam Musa Alkazim (as) wacce akewa alkunya da (ma’asuma) amincin Allah ya kara tabbata gare ta.
- muhadara » Kyawawan halayen likita ne a muslunci
- muhadara » tsari daga sharrin Iblis
- muhadara » Ayoyin samun nutsuwa
- muhadara » Mace da tawayarta
- fikihu » Falalar ilimi da malamai
- fikihu » Sakon ziyarar arba’in cikin iraki-tattaunawa tare da samahatus sayyid Sami badari.
Maganar mu cikin kur’ani da saukarsa kan zuciyar annabi mafi karamci (s.a.w) domin ya kasance mai bushara da gargadi daga ubangijin mai rainon talikai, daga cikin mutane akwai masu ganin kur’ani ya sauka kamar misalin saukar ruwan sama daga nesa-nesa, ma’ana cikin saukarsa ya kasance yanki-yanki a yayyanke daga nesa-nesa, idan ya kasance a samaniya, lallai bai kasance tsakankanin mutane ba sai bigirensa ya zama nesa-nesa mai wofinta, idan ya kasance a doron kasa tsakankanin mutane, lallai shi bai kasance a samaniya ba cikin madaukakan halittu, shi nesa-nesa idan aka auna shi da kasa to ya na samanta ne haka akasin haka, bayan saukar kur’ani daga masdarinsa da farko da sannu zai yanke, a wannan lokaci kuma masu tafsirinsa suke fara tafsirin kur’ani irin tafsirin duniyar kasa shimfidadda, hannu duniyar kasa bai iya kaiwa ga yin tafsirn duniyar sama ta al’arshi, misalin wannan tafsiri ga kur’ani da sannu zamu shaki kamshin tafsirin duniyar kasa da turbaya kai hatta ko da ya zurfafa bincike cikinsa, lallai kamar misalin wanda ya yi nutso ne cikin tafki domin ya fito da gwalagwalai, sai dai cewa tafki na wanzuwa a ban kasa daga kasa, sai tafsiri a wannan lokaci ya kasance ya yanko daga sama ya damfaru da kasa amma a wajen masu dandake bincike daga malamai bayin Allah nagargaru lallai shi saukar kur’ani mai girma kadai dai shi ya sauka ne da yanayin igiya mikakka mara yankewa daga sama, bari gefe guda na hannun Allah matsarkaki daya barin gefan kuma na hannun mutane, lallai shi daga tajalli yake bai kasance daga nesa-nesa ba nesanta, sai ya sauka daga wajen Allah matsarkaki madaukaki da haruffansa da lafuzzansa da ma’anoninsa a kan zuciyar tsarkakka ga saukar igiya mikakk, duk wanda ya yi riko da shiya tsira ya `daga zuwa sama, kamar misalin wanda ya yi riko da igiya mikakka domin fitowa daga cikin rijiya da ya fada cikinta, sannan ya `daga da shi zuwa sama, ga ubangijinka inda magaryar tukewa ta take, duk wanda ya yi imani da wannan ya kuma nufi tafsiri da yin sharhin kur’ani mai girma, to fa lallai shi kari kan tafsrinsa na kasa lallai zai tafsirinsa irin tafsirin sama na malakutiya daga al’arshi ubangiji mai rainon bayi, a wannan lokaci banbanci nawa ne tsakanin tafsiran guda biyu na sama da na kasa, banbanci nawa ne tsakanin sauka irin ta ruwan sama da kuma irin ta mikakkiyar igiya (tajalli) da (nesa), shi kur’ani mai girma igiya ce karfaffa, kuyi riko da igiyar Allah baki daya kada ku rarraba, lallai Allah ya rataye shi tsakaninsa da tsakankanin bayinsa, wannan igiya bata kasance yankakkiya ba kamar misalin igiya da ta yanke ta fada gidan wani mutum, lallai shi ba zai samu dagawa ba zuwa madaukaka, bari dai daga igiya mikakka gefe guda da yake hannun Allah da iliminsa da ikonsa da rayuwarsa.
Shin saukar kur’ani sauka ce irinta ruwan sama daga nesanci da ma’anar kasantuwa daga sama, bai kasance kasa ba haka ma akasin hakan, ko kuma shi daga sauka irinta igiya daga tajalli wanda amirul muminina ali (as) cikin nahjul balaga inda yake cewa:
(فتجلّى لهم سبحانه في كتابه من غير أن يكونوا رأوه).
Sai ubangijin matsarkaki ya yi tajalli garesu cikin littafinsa ba tare da ya kasance sun ganshi ba.
Duk wanda da farko tafsirinsa daga kasa ya kasantu to duk yarda ya kai ga zurfafa kamar misalin zurfafar kogi, sai ka kamsashi kamshin turbaya da kasa da launantu da launin kasa da fatarsa mai launi-launi. Idan aka ce shi ruwa cikin saukansa da tattararsa yana zama tafki, kamar yadda tafki yake da sama da zurfi, zahiri da badini, duk wanda ya ga tafki, lallai shi wani lokaci samansa da zahirinsa, wani lokacin kuma zurfinsa da badininsa, sai muce idan hakan ya kasance ya kasance daidai ya inganta sai dai cewa duka biyun suna tukewa zuwa ga kasa, lallai shi tafki daga kasa yake gareta yake komawa, kamar yadda kake gani cikin misalin tafsirin fakruz razi da jarullahi zamakshari da wanda ya kasance da irin tunaninsu, ya yinda da suke ganin saukar kur’ani daga irin misalin saukar ruwan sama ba tare da bayan saukar ya sadu da sama daga duniyar badini da jabruti ba. Amman wanda yake ganin cewa saukarsa daga irin mahangar saukar mikakkiyar igiya ce mai saduwa da hadewa kamar misalin ayatollah husaini taba’taba’I a cikin tafsirinsa mai suna almizan fil tafsiril kur’an, lallai shi zaka shaki kamshin malakutiyya badini daga gareshi, ya nada zahiri kamar yadda yake da zurfafa mafi girma cikin tawilinsa, kadai dai wanda dai yake sanin kur’ani shi ne wanda aka saukarwa kur’anin akai magana da shi da kur’anin, kamar yadda kake kamsasar kamshin kasa daga gareshi, ka ga haskayen al’arshi, kamar yadda ya kasance daga tafsirin mala’ikanci da shuhudi daga tafsirin badinin da gaibu.
Daga wanda yake tafsirin kur’ani wani lokaci ya kanyi tafsirinsa daga wajen Allah na farko yana daga tajalli na biyu kuma daga nisanci.
Na farko yana ganin cewa dukkannin ni’imomi daga wajen Allah matsarkaki suke
﴿وَمَا بِكُمْ مِنْ نِعْمَةٍ فَمِنْ اللَّهِ ﴾.
Babu wata ni’ima da take gareku face daga Allah take.
Kamar yadda yake ganin cewa lallai abin da yake cikin doran kasa na daga runudunonin Allah
﴿وَلِلَّهِ جُنُودُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ﴾.
Ga Allah rundunonin sammai da kasa suke.
Sai ya ga kasa sai dai cewa ita tana rataye tanada alakantuwa da sama, da abinda ke amfanar da mutane da al’umma cikin tafsiri da tawili ga kur’ani mai girma da abin da ya kasance mahangar mai tafsirin dangane da saukar kur’ani daga misalin mikakkiyar igiya mara yankewa daga Allah matsarkaki, lallai duka wanda ya yi riko da shi daga wadanda Allah ya karesu ya tseratar da su domin ismarsa da tabbatuwar ilimi da ma’arifa da daukaka cikinsa, ya kasance misdakin abin da riwaya ta zo cikinsa (karanta ka daukaka) ma’ana da iliminka da riko da igiyar darajarka zata daukaka ta `daga zuwa ga aljannar Firdausi madaukakiya tare da makusanta cikin aljanna korama cikin matsugunin gaskiya wajen sarki mai ikon yi, duk wanda yake da ittisali da dangantaka da sama da iko mudlaki mara kaidi da ilimi mudlaki mara kaidi da rayuwa mudlaka wacce take daga siffofi na zati da subutiya ga Allah madaukaki matsarkaki kada ya debe tsammani daga rahamar Allah, kamar yadda kada ya yi magana da debe sarai da munanawa da abubuwa marasa kyau, bari dai kowanne lokaci ya kamata ya rayu cikin kyakkyawan fata da rahama da nishadi, sannan kur’ani da tsarkakakken tsatso hakika ce kwaya daya daga wanda shi daya ne dayantacce ubangijin masu raino girmansa ya girmama. Babu shakka duk wanda ya kasance daga ahalin wannan hakika, lallai shi zai kasance ma’abocin dayanta Allah a zahirinsa da badininsa zai yi kira zuwa ga Kalmar tauhidi da kuma hada kai. Zai hada kan al’umma da jama’a.
Sannan ka sani lallai sabani da rarrabuwa da kungiyanci da bangarori wani lokaci daga kasa tsakanin ahlin kasa, to wannan zai iya yiwuwa a magance shi da dinke barakarsa da hada zukata sahu-sahu hakan na kasancewa ta hanyar wa’azi da nusantarwa daga masu kawo gyara cikin al’umma da ma’abota addini cikin warware matsaloli da sabani da kawar da rigingimu da jayayyar daidaiku da ta jama’a da dinke Baraka da hada kawuka sahu-sahu.
Sai dai cewa yana kasancewa sababin sabanin da rigima da juna da kiyayya da gaba daga abin da sama ta wurgo daga Allah madaukaki matsarkaki, to fa maganin wannan bai kasancewa misalin yin wa’azi ba kadai, bari dai ya zama tilas a komawa Allah ayi masa magiya da kan’kan da kai da kuka zuwa gareshi matsarkaki har ya dauke bala’in da fitintunun da musibu daga kafadun mutane lallai wannan sabanin da sassabawar na daga azabar Allah, kadai wani lokaci yana kasancewa ta fuskanin wurgowa wani lokacin kuma da yanayin cune kamar yadda ke cikin surar ma’ida dangane ga yahudawa da nasarawa, lallai tare da yahudawa ya bayyana sabaninsu da rigima da juna da yanayin wurgowa kamar yadda ya zo cikin fadinsa madaukaki:
﴿ وَأَلْقَيْنَا بَيْنَهُمْ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاءَ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ ﴾.
Muka wurga kiyayya da gaba tsakankaninsu har zuwa ranar kiyama.
Amma dangane da nasarawa kiristoci to bayanin ya zo kansu da yanayin cune.
﴿ فَأَغْرَيْنَا بَيْنَهُمْ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاءَ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ﴾.
Sai muka cuna adawa da keta tsakaninsu har zuwa ranar kiyama.
Cikin wata ayar daban ishara ta zo ga asalin azabar da saukarta daga sama daga kasa sai Allah madaukaki yace:
﴿قُلْ هُوَ الْقَادِرُ عَلَى أَنْ يَبْعَثَ عَلَيْكُمْ عَذَاباً مِنْ فَوْقِكُمْ أَوْ مِنْ تَحْتِ أَرْجُلِكُمْ أَوْ يَلْبِسَكُمْ شِيَعاً وَيُذِيقَ بَعْضَكُمْ بَأْسَ بَعْض﴾.
Ka shi mai iko ne kan aiko da azabba kanku daga samanku ko kuma daga karkashin kafafuwanku ko ya gauraya ku kungiyoyi ya dandanawa sashenku musibar sashe.
Azaba mai sauka daga sama a wani lokaci tana zuwa misalin walkiya mai konewa, wani lokacin kuma misalin azaba tsakankaninsu, itace mafi tsananin azaba daga ta farko. Duk wanda yake ganin kur’ani ya sauka misalin mikakkakiyar igiya da kuma tajalli daga Allah matsarkaki, to lallai shi babu makawa zai yi kira cikin maganganunsa da nusantarwarsa ya zuwa hadin kai tare da kashe-kashensa musammam ma hadin kai na muslunci a kebance kuma hadin tsakankanin `yan shi’a, domin su zauna kan walimar Allah mai girma da daukaka wacce walimar nan itace kur’ani wacce Allah ya yi tajalli cikinta da girmansa da kyawunsa da kamalarsa.
Ina hada ku da Allah kan hadin kai da hada kawukan musulmi da muminai, ina hada ku da Allah kan hadin cikin dayanta Allah da hadin kan mutumtaka.
Idan kuma kuka ki yi to ku sani lallai shi sabani da rigingimu tsakankanin muminai kadai dai shi sabani tsakankanin muminai azaba ce daga Allah matsarkaki, azaba daga samanku daga karkashin kafafuwanku.
﴿ يَلْبِسَكُمْ شِيَعاً وَيُذِيقَ بَعْضَكُمْ بَأْسَ بَعْضٍ ﴾
Kuma ya gauraya ku kungiyoyi ya kuma dandanawa ba’arinku azabar ba’ari.
Sai dayanku ya kafirta dayanku ya tofa miyau a fuskarsa kamar yadda ya zo cikin hadisan tankada da rairaya, cikin karshen zamani musulmi zai tofa miyau a fuskar dan’uwansa musulmi. kamar yadda hakan ya zo cikin hadisan tankade da rairaya a cikin karshen zamani wannan yana daga cikin mafi tsananin azaba kan al'umma cikin rasa kyautata zato da rashin aminci tsakankanin junansu, kowannensu yana bugun dan'uwansa yana cin namansa, kungiyoyi su dinga jifan juna da bangaranci a tsakaninsu, Allah ya sanya azabarsu tsakaninsu alhalinsu su suna daga al'umma guda daya kan mazhaba daya.
Duk wanda ya kasance ma'abocin tauhidi ciki badininsa da zuciyarsa lallai shi zai bayyana shi cikin maganganunsa da da'awarsa cikin zantukansa da ayyukansa, sai ya zamanto yana kira zuwa ga hadin kai da daidaita juna. Daga cikin zamantakewa da juna da rayuwa da juna cikin zaman lafiya da kyautata zama waje guda shi ne kiyaye hakkokin ragowar mutane da rashin cutar da `yancinsu na mutuntaka, amma wanda ya kasance mushriki cikin zuciyarsa da badininsa, lallai hakan zai bayyana cikin fuskarsa cikin maganganunsa wadda bayanta akwai sassabawar mutane da rarraba su zuwa bangarori da kungiyoyi azabarsu tsakanin junansu.
Ma'abocin tauhidi a hakika bai ganin mutum matsayin dabba mai magana kamar yadda masana ilimin mandiki sukai bayaninsa haka, bari dai yana ganinsa rayayye mai imani da Allah sai ya zama yana alakanta shi da rayuwar Allah matsarkaki da sama, ya komar da shi zuwa asalinsa da ma'adanarsa, lallai ruhinsa daga duniyar badini daga sama kamar yadda ya zo cikin fadinsa madaukaki:
﴿وَنَفَخْتُ فِيهِ مِنْ رُوحِي﴾
Na yi busa cikinsa daga ruhina.
Ruhi mala'ika ne mai girma da ya fi jibrilu girmama ana kiransa da sunan ruhil mukaddas ko akdas shi yana daga malakut mafi daukaka,
﴿ آمَنُوا اسْتَجِيبُوا لِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ إِذَا دَعَاكُمْ لِمَا يُحْيِيكُمْ ﴾
Ya ku wadanda sukai imani ku amsawa Allah da manzonsa idan suka kiraku zuwa ga abin da yake rayaku.
Suna kiranku zuwa ga rayuwa madawwamiya ta har abada ba ta yammaci ba ko gabashi, bari dai igiya mikakka daga Allah matsarkaki ga wanda ya yi riko da ita
﴿وَاعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللَّهِ جَمِيعاً وَلا تَفَرَّقُوا﴾.
Kuyi riko da igiyar Allah baki daya kada ku rarraba.
Lallai Allah yana so masu riko da karfaffiyar igiyarsa da kur'aninsa mabayyani da Muhammad da iyalansa tsarkaka, karshen zancenmu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai.
Bawan Allah sayyid adil alawi
15 ga watan Ramadan shekara ta 1438