lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Tambaya a takaice: kasantuwar ya zo cikin hadisi cewa hazrat Fatima (as) a wata rana bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) tayi shaukin ganin Salmanul farisi sannan Fatima lokacin haduwarta da Salmanu ta sanya gajerun kaya, yaya za ai bayani kan wannan hadis

, sai nace ya masoyiyata ni banyi muku jafa’i ba, sai tace yi shiru zauna ka hankalci abin da zance maka… sai tace kayi bude baki kan wannan danyen dabino sannan idan kiyama ta tsaya gobe ka zo mini da kwallonsa.

Da farko bisa zahirin wannan hadisi hazrat Fatima tai shaukin ganin Salmanu wand ashi ba muharraminta bane ta kuma so ganinsa, me yasa hakan? Sai dai cewa a sani nifa bawai ina son kore ma’asumancinta ba ina neman tsarin Allah daga haka, amma kuma mene ne ya sanya macenta da take bar koyi cikin kamewa da kunya kai hatta gaban makaho tana sanya hijabi amma kuma ace anan zuciyarta na begen ganin wanda ba muharraminta ba? duk da cewa wannan wand aba muharramin ba mutum misalin Salmanul farisi, na biyu mai girma Salmanu da kansa yake cewa cikin wannan hadisi duk sanda hazrat zahara ta nemi lullube kanta da abayarta sai kwaurinta ya yaye hakama duk sanda ta nemi rufe kwaurinta da abayar sai kanta yaye, ma’ana dai a wannan waje shi mai girma Salmanu ya ga kwaurinta ya kuma ga kanta, me ya sanya hakan? Ko kuma misali mu ce shi mai girma Salmanu daga bangaren manzon Allah (s.a.w) da sarkin muminai Ali (as) aka tura shi zuwa gidan hazrat Fatima domin ta gaya masa wani lamari, ok shin cikin wannan hali ba zai yiwu ba ta wata hanyar ba wannan lamari ya zo gareshi ta yadda za a aminta da ganin junansu tunda su ba muharraman juna bane? 

Amsa a takaice:

1-kasancewar hazrat Fatima (as) tayi shaukin ganin Salmanul Farisi bai wata matsala da ma’asumancinta saboda da za ka lura da farkon hadisin da hakama da karshensa zaka fuskanci cewa wannan haduwa da sukai ta kasance bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) sannan zaka ga cewa imam Ali da Fatima suna cikin kwanakin bakin ciki da zaman makoki da jimami suna kauna da begen cewa Salmanul farisi da kasance da wancan girmama da hatta manzon Allah (s.a.w) cikin hakkinsa yana cewa (salmanu daga garemu yake Ahlil-baiti) ya kamata yayi saurin riskarsu yaje wajensu ya yi tarayya dasu cikin bakin cikinsu.

2-hazrat zahara (as) cikin kowanne irin yanayi da wuri da wanda ba muharraminta ba tana kiyaye hijabi da kamewarta, tare da lura da wannan gaba, shi Salmanu yana cikin mukamin siffanta tufafi ne wanda ku nuna saukin kan hazrat zahara (as) ba wai ya nuna cewa hakika shi ya ga kwaurinta kafarta ba tsirara wanda ya kamata mu nemi tsarin Allah daga tunanin faruwar hakan gareta, sannan kari kan haka riwayoyi sunyi bayani karara kan cewa mataye ma’abota addini a wancan zamani suna kasancewa a karkashin abayar da suke sanyawa akwai dogon wando da yake kaiwa har dunduniya, saboda haka ita ma hazrat zahara (as) tana sanye da wanda da ya rufe dukkanin kafarta cikin wannan gajeriyar abaya.

Amsa dalla-dalla:

Riwayar da take da alaka da haduwa Slmanul farisi da hazrat zahara (as) wacce aka kawota kan wancan tambaya- a wasu litattafan shi’a an nakalto ta daga cikinsu akwai littafin muhujul da’awat da minhajul ibadat na wallafar sayyid ibn dawus wanda yayi wafati a shekara 664 hijri wanda isnadin wannan riwaya ya kasance kamar haka: daga shaik Ali bn Abdus-samad ya ce shaik kakana ya bamu labari ya ce masanin fikihu Abu Hassan Allah ya jikan rai ya bamu labari ya ce: sayyid shaik Alimi Abu barakat  Ali bn Husaini hasani aljauzi ya zantar damu ya ce shaik Abu Jafar muhammad bn Ali bn Husaini bn Musa bn babawaihi kummi masanin fikihu (ks) ya zantar damu ya ce: Hassan bn muhammad bn Sa’id kufi ya zantar damu ya ce: Furatu bn Ibrahim ya zantar damu ya ce: Jafar bn muhammad bn bishrawaihi kaddanu ya zantar damu ya ce: muhammad bn Idris bn Sa’id Ansari ya zantar damu ya ce: Dauda bn Rashid da walid bn shuja’u bn marwanu daga Asimu daga Abdullah bn Salmanu farisi daga babansa ya zantar damu ya ce:[1]

Wannan riwaya ce mai tsayi wacce a wannan mahalli d amuke ciki kadai za a tarjama iya inda akai tambaya kansa: ya zo cikin riwayar cewa: salmanu farisi yana cewa: kwanaki goma bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) na fito daga gida na nufi gidan hazrat fatima (as) sai Ali ya ce mini” ya kai salmanu kai bayan wafatin manzon Allah kai mana jafa’i ya masoyina ya Abu hassan ni banyi muku jafa’i ba, sai dai cewa bakin ciki da jimamin rashin manzon Allah (s.a.w) ya ya hana ni zuwa ziyararku, sai hazrat Ali ya ce mini: ya kai salmanu taho mu tafi gidan fatima yar manzon Allah; saboda ita tana son yi maka wata kyauta kuma yana begen ganinka tana son baka tsarabar da aka kawo mata daga aljanna,  salmanu yana cewa: sai na nufi gidan fatima bayan na shiga cikin gidan sai naga fatima zaune sannan tana lullufe da wata yankin abaya sai dai cewa abayar duk sanda ta yunkura jawota kan kwaurin kafarta kanta zai yaye hakama duk sanda ta jawota kanta sai kwaurinta ya yaye, lokacin da ta ga salmanu sai ta lullufe kanta da wannan abaya, sannan hazrat fatima tace: ya kai salmanu hakika kai tun bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) kai mana jafa’i ko? Sai nace: ya ke yar manzon Allah, shin zai iya yiwuwa ace ni nayi miki jafa’i? Fatima(as) tace to zauna ka saurari abin da zan gaya maka ka hankalce shi sosa.[2]

 

Idan ana son samun ingantacciyar fahimta daga wannan riwaya dole a nutsu a lura da wadannan nukdodi:

1-ba’ari daga marawaitan wannan riwaya mutane da ba ‘a ma san sunayensu ba a litattafan ilimin rijalul hadis saboda haka riwayar isnadinta ba ingantacce bane.[3]

2-wannan riwaya ibn dawus ya kawo tane a babin cewa hazrat zahara (as) ta baiwa salmanu wata addu’a ne don kariya daga zazzabi[4] ana kiransa da sunan (hirzun hazrat fatima)[5]

Na uku: batun cewa fatima tayi shaukin ganin salmanul farisi, bai wani matsala da ma’asumancinta da kamewarta; saboda idan da ka lura da farkon hadisin da karshensa zaka fuskanci cewa lallai wanni haduwa ta faru bayan kwanaki goma da wafatin manzon Allah (s.a.w) sannan imam Ali da hazrat zahara (as) sakamakon wannan babban rashi da bakin ciki zuciyarsu ta shiga kadaici sai ya zama suna begen ganin salmanu, wanda ya kasance bain girmama d akauna tare da manzon Allah (s.a.w) da yadda ya samu kusanci dasu wanda ya kai ga da suna kirga shi daya daga cikin danginsu har ta kai ga manzon Allah yana ce masa (salmanu daga garemu yake Ahlil-baiti)

Sai yayi sauri ya tafi ganinsu domin yayi tarayya da su cikin bakin cikinsu da kadaicinsu, ta wannan fuska a lokacin da hazrat Ali (as) ya ga salmanu sai yayi sahukinsa ya ce masa ya salmanu kai bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) kai mana jafa’i ne? Sai salmanu daga wannan lokaci ya fadaka cewa fatima (as) ma tana begen ganinsa ta na kuma son bashi wata tsaraba da aka kawo mata daga aljanna, saboda haka ta wannan shauki da bege ta fuskar shari’a bai da wata matsala.

 

Na hudu:  idan kayi duba tare da lura zaka ga an nakalto cikin tarihi da sira tsari da shakalin hijabin da tufafin hazrat Fatima (as) zaka iya kaiwa ga wanna natija cewa ita a kowanne lokaci tare da wand aba muharraminta ba tana cikakken kiyaye hijabi da tufafinta, sai dai cewa tana kiyaye matsakaicin haddi wanda hakan wani abin koyi ne ga sauran matan musulmai. Bisa la’akari da wannan nukda daga bangaren da ya zo a riwayar da cewa (sai kwatsam na sameta zaune kanta akwai wani kyalle daga abaya wacce idan ta lullube kanta kwaurinta zai yaye idan kuma ta rufe kwaurunta kanta zai yaye)ya kamata ace salmanu kadai dai yana bayanin kaya ne wand ayake nuna saukin kan hazrat Fatima (as) bawai hakika kwaurin kafarta ya kasance tsirara, Allah ya tsare mu daga wannan tunani. Kari kan wannan bayani ya zo a riwayoyi da dama cewa mataye gama gari a wancan zamani suna sanya dogon wando kasan abayarsu manzon Allah (s.a.w) yana cewa: (Allah yayi rahama ga macenta da take rufe kafafuwanta take sanya wandon kirki)[6] da wannan siffantawa ta kaka za ace hazrat zahara (as) wacce take tare da da mukamin isma da kamewa da jin kunya ace ba zata sanya wannan dogon wando kasan abayarta da take gajeriya? Saboda haka tabbas kasan wannan abayan tana sanye da wani tufafi ba?!

Da lura da wadannan nukdodi cikin sauki zamu iya banbancewa tsakanin shauki da koyar da addu’a cikin abin da ya zo cikin tambayar, sannan ya kamata mu san cewa wasu sunyi mummunar fahimta daga hadisin ta yadda basa kiyaye hukunce-hukuncen shari’a tsakaninsu da muharrami da wanda ba muharraminsu ba, tabbas wannan kiyasi da suke gurbatacce ne.    

 

 



Dubawa da gyara kermani [1]   Muhujud da’awat . minhajul; ibadat: sh 5-6 wallafar ibn dawus Aliyu bn musa

[2] Muhujud da’awat. Minhajul ibadat wallafar ibn dawus Ali bn musa sh 5-6. Biharul anwar juz 43 sh 66 manakib sh 297-298

 

[4] Tambaya mai lamba 28424

[5] Muhujud da’awat: 5 hirzu maulatina fatima alaihas salam

[6] Manla yahaduruhl fakihu juz na 3 sh 467

Tura tambaya