lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

halayen jagora


Daga cikin abinda yake kan jagora shine bada umarni kuma dole jama’a su bishi inda zai ba da umarni kuma ba za a bishi ba shine kawai inda umarnin nasa ya sabawa Allah, anan ba za ai masa biyayya ba za a bishi ba, amma cikin dukkanin abinda yake na maslahar kasa na kawuka na cigaban kasa idan ya bada umarni wajibi abi shi sannan kuma ya tsaya kai tsayin daka kan biyayyarsa wannan ba girman kai bane, saboda tsayawarsa tsayin daka kan binsa gyaran kasa ne umarni ce, lokacin da imam Ali (as) ya aika Mailkul Ashtar misara me ya ce, haka ma lokacin da ya aika wasu kwamandoji biyu nasa zuwa ga Malikul Ashtar me ya ce,

وقد أمرت عليكما وعلى من في حيزكما     

Na sanya jagorancin Malik bn Ashtar kanku da kan wadanda suke tareda kanku

Ku ji maganarsa kuyi masa biyayya ku sanya shi sulke da garkuwa.

Dole ne su bishi tareda cewa amincin Allah ya kara tabbata gareshi yace: (babu da’a ga wani mahaluki cikin sabon mahalicci) amma sai yace wajibi ne suyi biyayya ga jagoransu, sai dai a matsayin na jagora me zaka ce ayi kowaye dole ka nemi abinda zai yiwu abinda zai iya kada ka dora masa abinda ba zai iya ba, shi ya sa ma imam (as) yake cewa:

إذا أردت أن تطاع فاسئل ما يستطاع.

Idan kana so ai maka biyayya da da’a to ka tambayi abinda za a iya.

Na biyu: idan kana sama kana bada umarni ga na kasa kana ku maso na kasa da kai ya bi ka to dole ne ka gyaru kuma dole kaima ka bi na sama da kai, kamar shugaban kasa ne idan yana son talakawansa su bi shi to dole ya zamo yana bin Allah, idan baka bin Allah baka tsoran Allah kada kayi tsammani na kasa da kai zai bika, imam Ali amincin Allah ya kara tabbata gareshi yana cewa:

أطع من فوقك يطعك من دونك.

Ka bi na samanka wanda yake kasa da kai zai bi ka.

وأصلح سريرتك يصلح الله علانيتك.

Ka gyara sirrinka badininka Allah zai gyara zahirinka

Idan kana bada umarni ana sabawa zaka samu matsala idan kana sabawa na samanka zaka samu matsala, kuma lallai abubuwa zasu lalace su rikice daga baya, kana minista shugaban kasa yana baka umarni kana sabawa to lallai zaka samu matsala.

الخلاف يهدم الرأي.

Tura tambaya