lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Siyasar muslunci zama na Arba’in da shida


Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Siyasar muslunci zama na Arba’in da shida 

Taken darasi: Daukar Mataki

Abubuwan da suke hana shugaba daukar mataki akwai kokwanto, akwai tsoro sai kuma son zuciyar mutane, sai abu na hudu da yake hana shugaba daukar mataki shine danginsa na kusa da shi wasu su kan zuwa wajensa wanda daga danginsa ne na kusa da shi sai su hana shi daukar mataki, za mu ga imam Ali (as) yayi fada kan wannan sosai yana cewa cikin fadinsa:

والزم الحق من لزمه من القريب والبعيد وكن فى ذلك صابراً محتسباً واقعاً ذلك في قرابتك حيث وقع واتق عاقبته .

Wannan gargadi kan wanda makusantansu matansu suke hana su daukar mataki suke halaka da basu da mace da ya fiye musu alheri, akwai gwamnan da matarsa ta halaka shi akwai shugaban kasa a najeriya da matarsa ta halaka shi zata zuga shi da yayi dukkanin abinda ya ga dama.

Abu na biyar wani lokaci shine izgili na masu sabani masu saba musu idan zai gyara za suyi masa izgili hakan sai ya hana shugaba yin gyara, ya kamata shi ya sani idan bai gyara ba Allah zai kawo wasu su yi gyara.

Na shida shi ne gudun surutun mutane meye surutun mutane shine mutane su dinga zaginsa alhalin shi yana gyara ne babu mamaki sai ya tafi ko ya mutu sannan su yi nadama su gane cewa gyara ya kasance yana yi, shi ya sa imam Ali yake cewa kada abinda mutane suke fada a kanka ya munana maka idan ya kasance kamar yanda suke fada hakan ne to wannan ya rage maka zunubi da ukuba idan kuma sabanin yanda suke fada to ka na da kyakkywa har ga Allah.

Amma fa wannan fa duk bayan ya dau mataki, wajibi shugaba bayan yayi tunani yayi shawara yanke ya dau mataki.

Tura tambaya