sababun makaloli
- fikihu » KARIJUL FIKHU 27 RABIU AWWAL 1441 H CIKIN TA'ARIFIN IJTIHADI A ISDILAHIN FIKHU TSAKANIN SUNNA DA SHI'A
- fikihu » KARIJUL FIKHU 5 GA WATAN RABI’U AWWAL SHEKARA 1441
- muhadara » GISHIRI CIKIN TAFIN HANNU
- muhadara » Malamai magada Annabawa_ kashi na 3 tarihin Shaik Abbas Qummi
- hadisi » Muhimman wasiyoyi uku daga Imam Sadik (as)
- fikihu » Bahasul karakul fikhu: fatawa halascin karanta surori biyu
- hadisi » KASHE KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALAYEN SU
- hadisi » Ashabul Ijma da siffofin hadisi
- hadisi » Sirri daga sirrikan Sayyada Fatima Ma’asuma (a.s)
- muhadara » Rigima da dauki ba dadi tsakanin hankali da wahami
- muhadara » kada ku kauracewa wannan kur'ani
- hadisi » Addu’a mabudin ibada
- muhadara » Mace da tawayarta
- muhadara » Nasiha ga masu shirin yin aure
- muhadara » Adalci hadafin daukacin addinai
makaloli
- fikihu » Bahasul karakul fikhu: fatawa halascin karanta surori biyu
- fikihu » siffofin jagora
- fikihu » Muna ta’aziyya ga daukacin al’ummar musulmi bisa munasabar tunawa da wafatin sayyada Fatima `yar imam Musa Alkazim (as) wacce akewa alkunya da (ma’asuma) amincin Allah ya kara tabbata gare ta.
- muhadara » Nasihar mahaifi ga dansa
- muhadara » Siyasar muslunci zama na Arba’in da shida
- fikihu » shin riwayoyin da suke cewa salmanu Farisi da Abu zar lokacin dawowar imam zaman (as) suna daga cikin matamaimakansa riwayoyi ne ingantattu
- fikihu » KAN HANYAR SHUGABAN SHAHIDAI IMAM HUSAINI (AS)
- muhadara » Karanta, yi tunani, ka yi aiki, ka san makiyinka Shaidan
- fikihu » Mujallar sautul kazimaini 222-221 watannin muharram mai alfarma da safar hijira ta shekaru 1439 wacce tayi daidai da 2017
- hadisi » Malamai sune magada Annabawa
- muhadara » Falsafa da siyasa cikin muslunci
- fikihu » siffofin jagora
- muhadara » Mace da tawayarta
- muhadara » Adalci hadafin daukacin addinai
- fikihu » Shin lazimtar wasu ba’arin Azkaru ba tareda ƙayyade adadi da niyyar samun biyan bukata keɓantacciya shi yafi ko kuma ƙayyadewa da iyakance adadi?
Mukalolin da akaranta dayawa.
- fikihu » Sirri daga sirrikan manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata gare shi da iyalansa-tare da alkalamin samahatus sayyid Adil-Alawi (dz)
- muhadara » Ta Yaya dalibi zai iya sanin gobensa
- hadisi » KASHE KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALAYEN SU
- hadisi » Sirri daga sirrikan Sayyada Fatima Ma’asuma (a.s)
- hadisi » Malamai sune magada Annabawa
- muhadara » KISSAR SOYAYYA
- fikihu » Ku tashi tsaye domin Allah
- fikihu » Hukunce-hukuncen muslunci
- fikihu » Muna ta’aziyya ga daukacin al’ummar musulmi bisa munasabar tunawa da wafatin sayyada Fatima `yar imam Musa Alkazim (as) wacce akewa alkunya da (ma’asuma) amincin Allah ya kara tabbata gare ta.
- muhadara » Kyawawan halayen likita ne a muslunci
- muhadara » tsari daga sharrin Iblis
- muhadara » Ayoyin samun nutsuwa
- muhadara » Mace da tawayarta
- fikihu » Sakon ziyarar arba’in cikin iraki-tattaunawa tare da samahatus sayyid Sami badari.
- fikihu » Falalar ilimi da malamai
Domin kasancewa mutum mai kwarjini tsakanin mutane, to ka da ka sake ka yi wata Magana kan wani abu face bayan ka tabbatar da ingancin tushen da aka samo shi..
Idan wani mutumi ya zo maka da wani labari to ka binciki labarin gabanin bayyanar da shi.
Ka nesanci jita-jita.. ka da ka dinga gasgata dukkanin abinda ake fadi kai hatta rabin abin da ka gani.
Idan Allah ya jarrabceka da makiyi ta ka kishiyance shgi da kyautatawa..
Ka tunkude da wacce tafi kyawu, lallai kauna na sauya kiyayya.
Idan kana son gane hakikar abokinka to ka yi tafiya tare da shi, lallai cikin tafiya hakikar mutum na bayyana zahirinsa ya yaye, labarinsa ya fito fili, me yasa ma ake kiran tafiya da (safara) ? ai domin tana yaye dabi’u da halaye ta bayyanar da su. Idan mutane su kai maka hujumi suka dira kanka alhalin kai kana kan gaskiy, ko kuma suka jefeka da suka, to kayi farin ciki, lallai su suna tabbatar maka da cewa kai mutum mai nasara mai tasiri, ai kaga babu mai kula mushen kare, kuma babu bishiyar da take shan jifa sai mai fitar da kayan marmari.
Ya kai dan dana lokacin da kake kalubalantar wani mutum, to ka yi sabo da idaniyar kudan zuma ya zamana da shi kake dubansa.
Ka da ka kalli mutane da idon kuda sai kallonka ya fada kan abinda yake kazantacce.
Sannan ya dana ka dinga kwanciya bacci da wurwuri.. albarka da ke cikin arziki tana cikin safiya, ina tsoratar maka ka da arzikin Allah ya fauce maka.. sakamakon kai kana kwana idonka bude ba tare da kayi bacci ba!
Ya dana ka tuna da hikayar kura da akuya don ya zamanto baka samu amintuwa da sakin jiki bag a wanda yake shirya makirci.
Sannan lokacin da wani ya yarda da kai to kada ka sake ka aikata ha’inci!
Zanje sarkakiyar Zaki. Zan sanar da kai cewa Zaki bai kasance sarki a daji ba don wai kurari, a’a ya kasance sarki ne sakamakon yana da kame kansa da mutuncinsa, bai yin kwace abin da waninsa ya farauto Duk inda ya kai da jin yunwa cikin na kunana!
Kada ka saci fafutikar waninka, sai ya zamanto ka aikata danniya da zalunci.
Zan tafi dakai wurin hawainiya domin da idonka ka ga yanda take dabara!
Ita fatar jikinta ta na launanta da wurin da ta samu kanta, domin ka san misalinta kwafi ne da take maimaici! Kuma ka san cewa akwai munafukai akwai kuma wasu mutane da suke lulluba da kowanne irin tufafi, suna kuma suturta da dukkanin da’awar alheri.
Ya dana ka sabawa kanka da yin godiya… ka godewa Allah!
Ya isheka ni’ima kasantuwa gashi kana tafiya kana ji kana gani!
Ka godewa Allah ka godewa mutane, lallai Allah yana karawa masu godiya
((وَإِذْ تَأَذَّنَ رَبُّكُمْ لَئِن شَكَرْتُمْ
لأَزِيدَنَّكُمْ))
والناس تحب الشخص الذي عندما تب
Lokacin da ubangijinku ya sanar tabbas idan kuka gode tabbas zan kara muku.
Mutane suna son mutumin da yayin da aka ni’imta shi zak kaskanta da kai yayi godiya ya girmama.
Ya dana ni na riga na gano cewa mafi girman daraja cikin rayuwa itace gaskiya!
Lallai karya ko da kuwa ta tseratar… to ita fa gaskiya ita tafi kamata da dacewa ga mutumin misalinka.
Ya dana ka samarwa kanka mayi kan kowanne irin abu..kayi tanadi da shiri cikin duniyarka kan kowanne lamari, don ya zamanto baka je kana magiya da rikon kafa ga kowanne kaskanrtacce ba, shi kaskantacce yana kaskantarwa yana kuma wulakantarwa!
Ka tyi kokari ka amfani kowacce dama daka samu, domin damar da ka samu yanzu ba lalle ne ta kara maimaituwa ba.
Kada ka dinga raki da kai kuka, ka zama mai juriya da fuskantar rayuwa!!
Ka gujewa mutane masu debe tsammani da shu’umai! Ka da ka sake ka zauna da dan canfi.
Ka da kayi dariya da murna da musibar da afku da waninka, ka da ka sake kayi izgili da sura da halittar waninka… babu wani mutum da ya halicci kansa.. lallai cikin izgilinka kana izgili ne kai tsaye ga wanda yayi halitta ya kaga ya suranta.
Ka da ka dinga tona aibobin mutane sai kaima Allah ya tona aibinka!
Allah shine mai yawna suturcewa, yana son mai suturce aibobin mutane..
Ka da ka zalunci kowa…
lokacin da karfin ikonka ya kirayeka kan zaluntar mutane to ka tuna da cewa Allah shine mafi karfin iko.
Idan wata rana ka ji kekasar zuciya to ka shafa kan maraya da sannu zaka ga abin mamaki yanda shafar kan maraya yake kawar da kekasar zuciya.
Kada kayi musu lallai cikin musu dukkanin bangarori biyu suna hasara!
Idan muka yi rashin nasara mun hasarar girmanmu
Idan kuma muka yi nasara to mun yi hasarar wani mutum!
Hakika dukkanin munyi rashin nasara.. da wanda yayi nasara da wanda ya yi zargin cewa bai yi nasara ba.
Ka da kasance mai kadai da ra’ayin kashin kanka abin da yafi kyawu shine ka tasirantu ka tasirantar, sai dai cewa ka da ka sake ka narke cikin ra’ayin wasu, idan ka tabbatar da cewa ra’ayinka shine yake kan gaskiya to ka tabbatu kansa ka da ka raurawa.