Mishkatu Fadima zahara

 

 
11
ـ في اُصول الكافي بسنده عن صالح بن سهل الهمداني قال : قال أبو عبد الله  7 في قول الله عزّ وجلّ : (اللهُ نُورُ السَّمَوَاتِ وَالأرْضِ مَثَلُ نُورِهِ كَمِشْكَاةٍ ) فاطمة  3 (فِيهَا مِصْبَاحٌ ) الحسن (المِصْبَاحُ فِي زُجَاجَةٍ ) الحسين (الزُّجَاجَةُ كَأنَّهَا كَوْكَبٌ دُرِّيٌّ) فاطمة كوكب درّي بين نساء أهل الدنيا (توقد من شجرة مباركة ) إبراهيم  7 (زَيْتُونَةٍ لا شَرْقِيَّةٍ وَلا غَرْبِيَّةٍ ) لا يهوديّة ولا نصرانيّة (يَكَادُ زَيْتُهَا يُضِيءُ وَلَوْ لَمْ تَمْسَسْهُ نَارٌ نُورٌ عَلَى نُورٍ) إمام منها بعد إمام (يَهْدِي اللهُ لِنُورِهِ مَنْ يَشَاءُ) يهدي الله للأئمة  : من يشاء (وَيَضْرِبُ اللهُ الأمْثَالَ لِلنَّاسِ ) والحديث طويل وفيه في تأويل قوله تعالى : (أوْ كَظُلُمَاتٍ )[1]  قال : الأوّل وصاحبه (يَغْشَاهُ مَوْجٌ ) الثالث (مِنْ فَوْقِهِ مَوْجٌ )

ظلمات الثاني (بَعْضُهَا فَوْقَ بَعْضٍ ) معاوية لعنه الله وفتن بني اُميّة (إذَا أخْرَجَ يَدَهُ ) المؤمن في ظلمة فتنتهم (لَمْ يَكَدْ يَرَاهَا وَمَنْ لَمْ يَجْعَلْ اللهُ لَهُ نُورآ) إمامآ. من ولد فاطمة  3 (فَمَا لَهُ مِنْ نُورٍ) إمام يوم القيامة[2] .

11-ya zo cikinusulul Alkafi da isnadinsa daga Salim bn Sahlu Hamdani ya ce: Abu Abdullah (as) ya ce: cikin fadin Allah mai girma da daukaka (Allah hasken sammai da kasa misalin haskena kamar taga) ai Fadima (cikin ta akwai fitila) Hassan (fitila cikin kwalaba) Husaini (kwalaba kai kace ita taurarone mai tsananin haske) Fadima ita tauraro ne mai tsananin haske tsakanin matan duniya (ana kunna shi daga bishiya mai albarka) Ibrahim (as) (zaituna ba bagabashiya bace ba kuma bayammaciya ba) ba bayahudiya bace ba kuma banasariya ba(manta ya kusa kusa haskawa koma wuta bata shafe shi ba haske kan haske) imami bayan imami (Allah yana shiryar da wanda ya so zuwa ga haskensa) ai yana shiryar da wanda ya so zuwa ga A'imma (Allah yana buga misalai ga mutum) hadisin yana matukar tsayi cikin sa tawili ne kan fadin Allah madaukaki (ko kuma kamar duffai) ya ce: duffai shi ne na farko da abokinsa (taguwar ruwa na rufe shi) shi ne na uku (samansa taguwar ruwa) Mu'awiya tsinannen Allah da kuma fitintinun banu umayya (idan ya fito da hannunsa) ai mumini cikin duhun fitintinunsu (bai kusa ya ganshi ba dukkanin wanda Allah bai sanya masa haske ba) imami daga `ya`yan Fadima (as) (bashi da haske) imami a ranar kiyama.

12 ـ في الدرّ المنثور: أخرج ابن مردويه عن أنس بن مالک وبريدة قالا : قرأ رسول الله  9 هذه الآية : (فِي بُيُوتٍ أذِنَ اللهُ أنْ تُرْفَعَ )  ، فقام إليه رجل

فقال : أيّ بيوت هذه يا رسول الله؟ قال : بيوت الأنبياء. فقام إليه أبو بكر فقال  : يا رسول الله  9 هذا البيت منها لبيت عليّ وفاطمة ؟ قال : نعم من أفاضلها  .

12-ya zo cikin durum Mansur; Ibn Mardawaihi ya fitar daga Anas bn Malik da Buraida sun ce: manzon Allah (s.a.w) ya karanta wannan ayar (cikin wasu gidaje da Allah ya bada izini a daga) sai wani mutum ya tashi gare shi ya ce: wadannan gidaje wadannan ya manzon Allah (s.a.w) ? sai ya ce: gidajen annabawa, sai Abubakar ya tashi gare shi ya ce: ya manzon Allah (s.a.w) wadannan gidaje shin daga cikin su lallai akwai gidan Ali da Fadima? Sai ya ce na'am suna daga cikin mafi darajarsu.[3]   

13 ـ عن جابر عن أبي جعفر  7 في قوله عزّ وجلّ : في بيوت أذن الله أن ترفع ويذكر فيها اسمه ، قال : هي بيوت الأنبياء وبيت عليّ  7 منها.

13-daga Jabir daga Abu Jafar (as) cikin fadinsa mai girma da daukaka: cikin wasu gidaje da Allah ya bada umarni a daga su a ambaci sunansa cikin su, ya ce: sune gidajen annabawa sannan gidan Ali (as) yana daga cikin su 

14 ـ عن مناقب ابن شهرآشوب بسنده عن أبي حمزة الثمالي : لمّا كانت السنة التي حجّ فيها أبو جعفر محمّد بن عليّ ولقيه هشام بن عبد الملک أقبل الناس يتسائلون عليه فقال عكرمة : من هذا؟ عليه سيماء زهرة العلم لاُقرينه ، فلمّا مثل بين يديه ارتعدت فرائصه ، واُسقط في أيدي أبي جعفر  7 وقال : يا بن رسول الله، لقد جلست مجالس كثيرة بين يدي ابن عباس وغيره ، فما أدركني ما أدركني آنفآ، فقال له أبو جعفر  7: ويلک يا عبيد أهل الشام ، إنّک بين يديي بيوتٍ أذن الله أن ترفع ويذكر فيها اسمه .

14-daga manakib ibn Shahru'Ashub da isnadinsa daga Abu Hamzatu sumali: a shekara da Abu Jafar Muhammad b Ali (as) ya yi hajji cikin ta kuma ya hadu da Hisham Abdul-malik cikin wannan shekara da taron hajji sai mutane suka fuskanto suna tambaya gameda shi sai Ikramatu ya ce: wane ne wannan da yake da alamar hasken ilimi lallai zanje in cudanya da shi? Yayin da Ikramatu ya zauna gabansa sai kafadunsa suka kama karkarwa, kwarjinin Ikramatu ya fadi gaban Abu Jafar (as) sai ya ce: ya dan manzon Allah (s.a.w) hakika ni na zauna majalisai masu tarin yawa na zauna majalisin ibn Abbas da waninsa, bai faru riskeni ba abin da ya riskeni dazu, sai Abu Jafar (as) ya ce kaiconka ya kai dan karamin bawan mutanen sham, lallai ka kana gaban daya daga cikin gidajen da Allah ya bada izinin daga su da ambaton sunansa cikin su.

15 ـ في زيارة الجامعة الكبرى : خلقكم الله أنوارآ فجعلكم بعرشه محدقين حتّى منّ علينا بكم فجعلكم الله (فِي بُيُوتٍ أذِنَ اللهُ أنْ تُرْفَعَ وَيُذْكَرَ فِيهَا آسْمُهُ ).

15- ya zo cikin ziyaratul kubra: Allah ya halicceku haskaye sai ya sanya ku cikin al'arshinsa kuna kewaye har ya mana tautayi daku sai Allah ya sanya ku (cikin gidaje da Allah ya bada izini a daga su a ambaci sunansa cikin su).

16 ـ في تفسير عليّ بن إبراهيم بسنده عن صالح بن سهل قال : سمعت أبا عبد الله  7 يقول في قول الله عزّ وجلّ : (أوْ كَظُلُمَاتٍ )[4]  فلان وفلان ، (فِي بَحْرٍ لُجِّيٍّ يَغْشَاهُ مَوْجٌ )، يعني نعثل (مِنْ فَوْقِهِ مَوْجٌ ) طلحة والزبير، (ظُلُمَاتٌ بَعْضُهَا فَوْقَ بَعْضٍ ) معاوية ويزيد وفتن بني اُميّة (إذَا أخْرَجَ يَدَهُ ) في ظلمة فتنتهم (لَمْ يَكَدْ يَرَاهَا وَمَنْ لَمْ يَجْعَلْ اللهُ لَهُ نُورآ) يعني إمامآ من ولد فاطمة  3 (فَمَا لَهُ مِنْ نُورٍ)، فما له من إمام يوم القيامة يمشي بنوره كما في قوله تعالى : (يَسْعَى نُورُهُمْ بَـيْنَ أيْدِيهِمْ وَبِأيْمَانِهِمْ )   قال : إنّما

المؤمنون يوم القيامة نورهم يسعى بين أيديهم وبأيمانهم حتّى ينزلوا منازلهم من الجنان  .

16-ya zo cikin tafsirin Aliyu bn Ibrahim da isnadinsa daga Salihu bn Sahal ya ce: naji Abu Abdullah (as) yana cewa: cikin fadinsa mai girma da daukaka: (ko kuma kamar duffai) ai wane da wane (cikin tafki mai zurfi da taguwar ruwa ke rufe shi) ma'ana na'asalu (samansa taguwar ruwa) dalha da Zubairu (duffai sashenta saman sashe) ma'ana mu'awiya da yazidu da fitintinun banu umayya (idan ya fto da hannunsa) cikin duffan fitintinunsu (bai kusa ya ganshi ba dukkanin wanda Allah bai sanya masa haske ba) ma'ana imami daga `ya`yan Fadima(as)  (bashi da haske) bashi da imami ranar kiyama wanda zai yawo cikin mutane da haskensa, kamar yadda ya zo cikin fadinsa madaukaki (haskensu a yawo a gabansu da damansu) kadai muminai ne wadanda haskensu zai dinga tafiya a gabansu da damansu har sai sun sauka masaukansu a aljannoni.

 

17 ـ البحار بسنده عن الإمام زين العابدين عليّ بن الحسين  8 أنّه قال : مثلنا في كتاب الله كمثل مشكاة فنحن المشكاة ، والمشكاة الكوّة فيها مصباح ، والمصباح في زجاجة ، والزجاجة محمّد  9، كأنّه كوكب درّي يوقد من شجرة مباركة قال : عليّ  7 (زَيْتُونَةٍ لا شَرْقِيَّةٍ وَلا غَرْبِيَّةٍ يَكَادُ زَيْتُهَا يُضِيءُ وَلَوْ لَمْ تَمْسَسْهُ نَارٌ نُورٌ عَلَى نُورٍ) القرآن (يَهْدِي اللهُ لِنُورِهِ مَنْ يَشَاءُ) يهدي لولايتنا من أحبّ

 

17-daga littafin bihar da isnadinsa daga imam Zainul Abidin bn Husaini (as) lallai cewa shi ya ce: misalinmu cikin littafin Allah kamar misalin mishkatu ne taga mune mishkatu, ita mishakatu wani dan rami da yake jcikin bango wanda cikin sa akwai fitila, fitila cikin kwalaba, kwalaba Muhammad (s.a.w) kai kace ita tauraro ne mai tsananin haske ana kunna shi daga bishiya mai albarka, Ali ya ce: (as) bagabashiya bace ba kuma bayammaciya bace manta ya kusa haskuwa koma da wuta bata shafe shi ba haske kan haske) ai kur'ani (Allah yana shiryar da wanda ya so zuwa ga haskensa) ma'ana yana shiryar da wanda yake so zuwa ga wilayarmu  

18 ـ ابن المغازلي الشافعي بإسناده إلى الحسن قال : سألته عن قول الله تعالى : (كَمِشْكَاةٍ فِيهَا مِصْبَاحٌ ) قال  المشكاة فاطمة  3 والمصباح الحسن والحسين  8 و(الزُّجَاجَةُ كَأنَّهَا كَوْكَبٌ دُرِّيٌّ) كانت فاطمة  3 كوكبآ درّيآ

من نساء العالمين (يُوقَدُ مِنْ شَجَرَةٍ مُبَارَكَةٍ ) الشجرة المباركة إبراهيم  7 (لا شَرْقِيَّةٍ وَلا غَرْبِيَّةٍ ) لا يهوديّة ولا نصرانيّة (يَكَادُ زَيْتُهَا يُضِيءُ) قال : يكاد العلم أن ينطق منها (وَلَوْ لَمْ تَمْسَسْهُ نَارٌ نُورٌ عَلَى نُورٍ) قال : ابنها إمام بعد إمام (يَهْدِي اللهُ لِنُورِهِ مَنْ يَشَاءُ) قال : يهدي لولايتهم من يشاء 

18- Ibn magazili bashafi'e da isnadinsa zuwa Hassan ya ce: na tambaye shi gameda fadin Allah madaukaki: (kamar taga cikin ta akwai fitila) sai ya ce: abin da ake nufi da mishkatu anan Fadima (as) sannan misbahu fitila sune Hassan da Husaini (as) (kwalaba kai kace ita tauraro ne mai tsananin haske) Fadima (as) ita ce tauraro mai tsananin haske daga matan duniya (ana kunna shi daga bishiya mai albarka) bishiya mai albarka shi ne Ibrahim (as) (ba bagabashiya ba kuma bayammaciya ba) ba bayahudiya b aba kuma banasariya ba (manta ya kusa haskawa) ilimi ya kusa magana daga gare ta (koma da wuta bata shafe shi ba haske kan haske) danta imami bayan imami (Allah yana shiryar da wanda zuwa ga haskensa) Allah yana shiryar da wanda ya da wilayarsu.

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah wanda ya sanya mu daga cikin masu riko da wilayar shugabar matan aljanna Fadaima Zahara da babanta da mijinta da `ya`yanta A'imma ma'asumai.

Karshen maganarmu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai.


[1] ()  الميزان :15 153.

[2] ()  النور: 40.

[3] Tafsirul nurul saklaini: m 3 sh 612.sannan kana iya komawa biharul anwar m 23 sh 304 babi na 18 ya yi bayanin cewa su A'imma hasken Allah ne sannan sune tawilin ayar nuru da kuma riwaya ta 42

[4] ()  المصدر: 31.