■ Watan Ramadan mai albarka jagoran watanni:
■ Muhadarar daren lailatul kadari na biyu
■ Siradi mikakke
■ Muhadarar daren lailatul kadari na uku
■ Cikin inuwar tafsrin kur'ani da tawilin ayar haske
■ amma mufradat din tafsirin ayatun nur haske
■ Mishkatu Fadima zahara
■ MUHADARA TA HUDU
■ Daga cikin abubuwa wadanda ayar nuru ta kebantu da su
■ Balagar kur'ani mai girma
■ ludufi na farko daga mishkat
■ Me ya sanya Fadima Zahara (as) ta zamanto tagar haske
■ Fadima Zahara ruhin annabi
■ Muslunci addinin ilimi da aiki
■ Sarkin muminai girman fahimta
■ Fadima Zahara kyawun Allah
■ Fadima Zahara uwar kyawawan abubuwa
■ Ludufi na biyu
■ Kafa dalili da suratul kadari kan imamanci
■ dalilai na fadimiyya wadanda muka kafa hujja da su kan halifacin sarkin muminai Ali
■ Daga siffofin Zahara
■ FADIN SHAHADA HUDU CIKIN KIRAN SALLAH DA IKAMA
■ FADIMA ZAHARA (AS) ABAR KOYI DA KWAIKWAYO
■ DAGA WAHAYIN ZIYARAR FADIMIYYA
■ WALKIYA DAGA HASKEN ZAHARA (AS)
■ MARUFINSA ALMISKI
ثمّ قال رسول الله 9: ولو كان الحسن شخصآ لكان فاطمة بل هي أعظم .
Sannan manzon Allah (s.a.w) ya ce: da ace kyawu mutum ne da ya kasance Fadima bari ma ita tafi girmama daga kyawu.
Idan Ali (as) ya kasance shi ne fikihu shi ne ilimi to lallai yadda al'amarin zai kasance Fadima itace kyau da kyawunta lallai ita tana tattaro baki dayan kyawawan akidu da dabi'u da hankali da ibada da hankaltuwa kai da dukkanin abin daya kasance cikin samuwar annabawa da wasiyyai da waliyyai da Mala'iku cikin da cikin sammai da kasa da cikin dabi'a da halittu da abin ya buyar daga gare su, lallai tsantsar kyau kyawu tsantsa shi ne Allah matsarkaki da sunayensa kyawawa da siffofisa madaukaka yana tajalli da kyawuntarsa da kyansa cikin fadima Zahara (as) lallai da Allah zai tattara dukkanin kyawu cikin wani mutum sannan ya busa masa rai to tabbas wannan mutum zai kasance Fadima amincin Allah ya kara tabbata gare ta.
Babu mamaki lallai wannan dandakakkun jumloli da suka zo cikin hakkin A'imma tsarkaka `ya`yan Fadima Zahara (as) kamar yadda ya zo cikin ziyara jam'a kubra wacce itace mafi ingancin isnadi da dilala da ishara da ya zo cikin ta:
(والحقّ معكم وفيكم ومنكم وإليكم وأنتم أهله ومعدنه وميراث النبوّة عندكم ).
Gaskiya na tare da ku taa cikin ku daga gare ku zuwa gare ku kune Ahlinta ma'adaninta kune wadanda gadon annabta ka wurinku.
Dukkanin abin daMala'iku suka sauko da shi wurin annabawa lallai shi taskace yake wurin A'imma tsarkaka: da dukkanin wani kyawu da za a ambata daga ilimi da hakuri da karamci na cikin ku, da dukkanin wata siffa mai kyawu cikin dukkanin duniyoyi lallai asalinta da farkonta da makurarta na wajansu
«إن ذكر الخير كنتم أوّله وأصله وفرعه ومعدنه ومأواه ومنتهاه ».
Idan an ambaci alheri sai ku kasance kune farkonsa asalinsa reshensa ma'adanarsa mafakarsa makurarsa.
Lallai sune ma'adanin alheri da asalinsa da matukarsa, jijiya da tushen dukkanin alherai a asalin kyawawan halaye baki dayansu da daukaka da girmama kadai dai suna cikin a'imma tsarkaka. Sannan dukkanin abnda ke gare su kadai dai daga mahaifiyarsu yake Fadima Zahara wacce itace ma'ajiyar fitilun shiriya kamar yadda ya zo cikin tawilin fadinsa madaukaki:[1]
(مَثَلُ الَّذِينَ يُنفِقُونَ أمْوَالَهُمْ فِي سَبِيلِ اللهِ كَمَثَلِ حَبَّةٍ أنْبَتَتْ سَبْعَ سَنَابِلَ فِي كُلِّ سُنْبُلَةٍ مِائَةُ حَبَّةٍ وَاللهُ يُضَاعِفُ لِمَنْ يَشَاءُ وَاللهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ ).
misalin wadanda suke ciyar da dukiyarsu cikin tafarkin Allah kamar misalin kwaya ce data tsirar da zangarniya bakwai cikin kowacce zangarniya akwai kwaya guda dari Allah yana ninkawa wanda ya so Allah mayalwaci ne masani.[2]
قال الإمام الصادق : الحبّة هي فاطمة الزهراء صلّى الله عليها، والسبع السنابل سبعة من ولدها سابعهم قائمهم .
Imam Sadik (as) ya ce: kwayar itace Fadima Zahara amincin Allah ya tabbata gare ta, zangarniya bakwai daga `ya`yanta na bakwansu mai tsayuwarsu.
Sannan zagarniyoyi bakwai sune A'imma daga `ya`yanta tun daga imam sadik har zuwa imam mahadi: kadai dai ya kebantu da wadannan tare da cewa hassan da husaini suma suna daga zangarniyoyinta; saboda iliman Zahara da kyawawanta kadai dai sun shahara sun yadu a cikin zamanin imam sadik har zuwa wannan zamanin namu da muke ciki.
Idan kwaya ba ta kasance ba ta kaka shuka zata kasantu? Ta kaka acikin manomi da nomansa zai kasance? Ita Zahara iatce kwayar shuka hakika Allah matsarkaki ya shukata, manzon Allah Muhammad (s.a.w) ya bata ruwa, sarkin muminai Ali (as) ya kula da ita, A'imma daga `y`yanta sune zangarniyoyi,sannan dukkanin wata albarka tana komawa asalintana, ma'ana kwayar, dukkanin albarkatun daga ma'abociayr albarka suke tsarkakka shugabar matayen duniya Fadima Zahara (as) A'imma zuriyarta da shi'arta zasu gajeta cikin dukkanin alheri cikin dukkanin kyawu da falala da alheri, da ace kyawu ya kasance mutum da ya kasance fadima bari dai itace mafi girmama,bari ita kanta tana aman kyau ba a hada ta dashi ba a kuma daidaita ta da shi, bari dai tana halittar kyau tana kagarsa tana kuma ceton masoyanta daga munanan halayedaga jahannama, kamar yadda cikin dalilin sanya mata sunan Fadima lallai ita tana yaye masoyanta daga wutar jahannama, tana kuma tsincesu cikin taro kiyama kamar yadda tsuntsu ke tsince lafiyayyen kwaya daga mara kyau, tana kuma kare shi'arta daga wulakanta lallai ita Fadima (as) mabayyanar kyau da kyawuntar Allah ce