Fadima Zahara uwar kyawawan abubuwa

 

Lallai itace mahaifiyar Hassan da Husaini da Muhsin, lallai itace mahaifiyar Zainab wacce itace adon mahaifinta sakin muminai (as) sai kyawun Fadima wada yake daga Allah ne ya yi tajalli cikin`ya`yanta rabutattu A'imma tsarkaka.

Ita Zahara mishkat ce ta kyawawa da falaloli fitilun Allah suna tajalli cikin ta, lallai Allah matsarkaki cikin suratun nuru ya bayyana mazubi da farko sanna a karo na biyu kuma ya bayyana abin daaka zuba cikin sa daga babin (ka fara tabbatar da samuwar kasa sannan sai kai zane cikin ta) sai ya bayyana Fadima Zahara da cewa itace mishkat mazubi, sannan ya bayyana annabinsa mafi karamci muhammadu (s.a.w) da cewar shi ne fitila, hakama A'imma goma sha daya daga `ya`yanta fitilun shiriya, me yafi kyawu daga wadannan jumloli na kur'ani cikin siffanta Fadima Zahara (as) ya bayyana da mishkata kamar yadda ya kira annabinsa da fitila, ya kira waliyinsa da kwalaba, yana nufin cewa ita tattaro kamaloli annabta da daukakr wilaya tsakankanin fukafukanta da cikin samuwarta, lallaiita tana tattaro dukkanin sasannin muslunci da sakonnin sama wadanda annabi ya zo da su wasiyinsa ya kiyaye su, haske da haskakauwarsa ta Allah mai huda yana tajalli cikin fadima domin ya haskaka duniya da al'ummu har zuwa tsayuwar kiyama, Zahara na nufin manzon Alllah da kur'aninsa da tsatsonsa tsarkaka.

Hakika ya zo cikin tawili da tafsirin suratul kadari da cewa lallai Fadima Zahara (as) itace daren lailatul kadari, kirjinta mai daraja da zuciyarta tsarkakka masauki ne mahalli ne na kur'ani da ake saukar da shi ciki, sai Allah ya saukar da kur'ani yana bayyana falalarta da darajojinta, kamar yadda ya saukar da shi domin Fadima Zahara (as) ta kasance mazubinsa, hakika masoyiyar manzon Allah ruhin zuciyarsa kadai dai ita mazubi ce ga mahaifinta da mijinta da `ya`yanta, kadai dai ita mahallin kur'ani ce mai daraja cikin tawilinsa da saukarsa cikin zahirinsa da badininsa cikin ilimansa da ma'arifofinsa, lallai ita lailatul kadari ce da aka jahilci matsayinta da falalarta da mukaminta.[1]

Lallai hakika kyawu baki dayansa da kyawunta baki dayansa yana bayyanuwa da Fadima, bari dai ita tafi girmama, a cikin bayanin girmanta akwai fuskoki: daga ciki shi ne lallai itace mafi daukakar sinadari, lallai mutum tun daga Adam da wadanda suka biyo bayansa kadai dai an haliccesu daga turbaya, sai dai cewa ita Fadima haura'u insiya lallai ana kiranta haura'u da ma'anar kamar matan aljanna sakamakon digon kwayar data samu ya fara kulluwa ne daga kayan marmarin aljanna kamar yadda ya zo cikin madaukakan hadisai masu tarin yawa-lallai itace mafi falalar sinadari, lallai ita sinadarin da aka samar da ita daga aljanna yake, manzon Allah (s.a.w) yana sumbatar kirjinta mai daraja yana cewa lallai ni ina jin kamshin aljanna.

Saboda haka samuwarta mishkat mazubi mahalli hasken Allah ne, lallai ita ismar Allah ce mafi girma kuma kwaryar kaddarar Allah da mashi'arsa da kur'aninsa mai magana, wannan tattarowa tata da yalwatarta ta samuwa shi ne abin da ake nufi.

 ludufi na farko daga mishkat.



[1] Ka koma ka nemi littafin durratul bahiyya fi asrarul fatimiyya cikin mujalladi na shida daga mausu'ar islamiyya na buga shi