Ludufi na biyu

: sannan daga cikin abubuwan da mishkat ta kebantu da shi shine cewa lallai ita tana kare fitila daga hatsarin tasowa da kadawar iska da mutuwa da bishewa, kai kace Allah   ya yi nufin cewa: hakika annabi mafi girma Muhammad (s.a.w) duk da cewa ya kasance cikin hatsarin mushrikai da kafirai da munafukai haka halifanci da imamanci na gaskiya a bayansa.

Suna nufin kashe hasken Allah da bakunansu Allah mai cika haskensa ne, wani lokacin da yake-yake na kishurwar zubar da jini da makamai masu kisan gilla wani lokacin kuma da magana, suna son bushe hasken Allah da bakunansu sai dai cewa shi Allah matsarkaki mai cika haskensa ne koda mushrikai da munafukai sun ki, lallai shi yana kare wannan haske na annabta da wilaya wanda aka danganta shi zuwa ga waliyyan Allah wadanda sune A'imma goma sha biyu- mishkat wani dan rami ne da yake jcikin bango, Allah mai cika haskensa ne wanda shi ne Ali (as) da `ya`yansa da wilayarsu da annabi da sakonsa da Fadima (as) wacce itace mishkat din haskayen tsarkaka, ba da ban it aba da makiya Allah sun bushe hasken Allah hasken sako da imamanci, sannan ya zo cikin madaukakin hadisi cikn siffanta annabi da tsatsonsa tsarkaka da shi'arsu rabautattu da bishiya da reshenta da ganyenta.

عن الإمام الباقر  7 :                                                     

الشجرة الطيّبة : رسول الله  9 وفرعها عليّ  7، وغصن الشجرة فاطمة  3، وثمرها أولادها، وأوراقها شيعتنا[1] .

Daga imam bakir (as): bishiya mai kyau: manzon Allah (s.a.w) rassanta Ali (as) reshenta Fadima (as) kayan marmarinta `ya`yanta (as) ganyenta shi'armu.

Sinadarin bishiya mai albarka wacce asalinta yake tabbace itace Fadima Zahara (as) ita ruwa ne rayayye , ba da ban ita ba da bishiyar bata yi kore ba da kayan marmarin basu nuna ba, rayuwar bishiyar da nunan `ya`yanta ya dogaro da sinadarin da ta samu, ba da ban Fadima ba da bishiyar annabta da imamanci ta bushe, da bata kore ba da bata nun aba da bata bada kayan marmari ba[2]

Muslunci ya tsayu da albarkaci zahara cikin samuwarta ta mala'ikanci ciki tsarin rayuwarta ma'asuma da maganganunta da jihadinta da zage dantsenta.

Sannan kur'ani mai girma cikin sa akwai ayoyi bayyanannu da masu kamanceceniya da juna, kadai dai masu kamanceceniya da juna sun bayyanu ta hanyar komarsu da su zuwa ga ayoyi bayyanannu cikin hujjoji masu huda da dalilai masu yankan shakku wadanda babu bukatar tattaunawa cikin kafa dalili da su.



[1] ()  المستمسک :5 544.

[2] Mustamsak: m 5 sh 545