Kafa dalili da suratul kadari kan imamanci

 

Daga cikin bayyanuwar suratul kadari, lallai ita tana daga cikin mafi bayyanar dalilai mafi cikar hujja tare da da wadanda suke jayayya da inkarin imamanci na gaskiya wacce ta misaltu cikin ahlil-baiti da tsatso tsarkakakke, kamar yadda A'imma sukai wasiyya da a kafa dalili da ita tare da abokan rigima, da a tambayesu da farko: shin lailatul kadari kwaya dace cikin tsawon  rayuwar duniya ko kuma ita kowacce shekara akwaita? Ba tare da wani kokwanto ba da sannu zasu ce cikin kowacce shekara akwai lailatul kadari, sai ka kara tambayarsu: shin wannan sura an shafeta ne? ba tare da wata shakka take zasu ce ba a shafeta ba sai ka kara tambayarsu: shin kan wane ne Mala'iku da ruhu suke sassaukowa cikin kowacce shekara cikin lailatul kadari a hannunsu kuma suna rike da tsarkaka?

Babu inda zamu a samu cikakkiyar wannan amsa sai wajen mazhaba ta gaskiya wacce tayi imani da imamanci da imamai goma sha biyu: na karshensu mai tsayuwarsu Mahadi Hujjatu bn Hassan Askari (as) lallai shi yana raye yana azurtuwa, dama samuwarsa ne kasa da sama suka tabbatu, albarkacinsa ake azurta mutane.

Da wannan imamanci da isma ke tabbatuwa ckin kowanne zamani.

Shugabarmu Fadima Zahara itace mishkat mahallin haske, itace lailatul kadari itace aya bayyananniya mai nuni kan annabta da imamanci itace mai kare haskensu har zuwa tashin kiyama.

 

Wani dan karin haske daga kafa dalili kan halifancin sarkin muminai (as)