Balagar kur'ani mai girma

 

Daga cikin balagar kur'ani mai girma shi ne cewa lallai uslubinsa da luggarsa kadai dai ya sauka kan tsarin:

 (إيّاکِ أعني واسمعي يا جارة )

Kai nake nufi ke kuma makociya ki jini.

Sannan lallai shi yadda al'amarin yake shi ne

 (الكناية أبلغ من التصريح )

lallai yin kinaya yafi fasaha daga bayyanarwa baro-baro.   

Da buga misali ga mutane tsammannsu sa tuna sayi tunani sa hankalta, daga wannan tunani ne muke ganin ishara zuw aga A'imma goma sha biyu cikin fadinsa madaukaki:

  (إنَّ عِدَّةَ الشُّهُورِ عِنْدَ اللهِ آثْنَا عَشَرَ شَهْرآ) ،

Lallai adadin watanni wajen Allah watanni goma sha biyu ne.[1]

Kamar yadda ya zo cikin madaukakan hadisai, jaka al'amarin yake cikin wasu ayoyin daban gameda imamancinsu da wilayarsu da saninsu.

Allah matsarkaki madaukaki shi ne hasken haskaye, mai haskaka haske, lallai shi ne hasken sammai da kasa, cikin mukamin misaltawa da surantawa da jikkanta wannan haske maficika mujarradi, lallai shi yana tajalli cikin mafi daukakar halittunsa Muhammad da iyalansa tsarkaka, lallai Allah wajibul wujud wanda samuwarsa take wajibi ga zatinsa cikin zatinsa da zatinsa, tsarki ya tabbatar masa mujarradi ne bai da jiki ya kuma tattaron baki dayan siffofin kyawu da jalala da kamala, sai da cewa shi yana tajalli da sunayensa da siffofinsa cikin halittunsa, sannan mai tattaron jam'in sunayen Allah kyawawa da sifofinsa madaukaka shi ne manzon mafi girma Muhammad (s.a.w) shi ne wanda ya fara gangarowa na farko shi ne mafi kamalar mutum shi ne ruhul A'azam, lallai Allah matsarkaki abin da ya fara halitta shi ne haskensa mafi tsarkaka shi ne fitila, sai dai cewa ita wannan fitila ta annabta wacce take cikin kwalaba wanda yake shi ne satrkin muminai Ali (as) kadai yana cikin mishkatu wacce ta ce Fadima Zahara (as) bayanin annabi da wasiyyi da sanin annabta da imamanci kadai dai yana yiwuwa da Fadima Zahara (as) kamar yadda ya zo cikin hadisil kisa'i hadisin bargo mai daraja, lokacin da Mala'iku suka tambayi ubangijin talikai kan cewa su waye suke cikin bargo, sai jawabi daga tushen jalala ya zo musu da cewa: (sune Fadima da babanta da mijinta da `ya`yanta) lallai ita ta tattaro haskayen annabta da Alawiyya, lallai ita `yar annabi ce matar wasiyyi mahaifiyar A'imma zababbu.

 

Sirrin kasantuwar Fadima zahara (as) mishkat

Kadai Allah matsarkaki ya kira Fadima da mishkat domin ludufai guda biyu: mai tattarowa da mai katangewa.



[1] Tauba:36