Me ya sanya Fadima Zahara (as) ta zamanto tagar haske

 

Amma me ya sanya Allah matasarkaki ya bayyana zababbiyarsa mabayyanar ismarsa da tsarkakarsa Fadima Zahara (as) da mishkat din haskaye? Domin lallai kamalar annabi mai tattaro kyawunsa da jalalarsa –ma'anar siffofin jamaliyya da jalaliyya-kadai dai yana tajalli cikin fadima Zahara (as) kamar yadda lafiyar fitila da kariyarta ke cikin kwalaba, haka annabi da siffofinsa na kamala kadai da su suna cikin fadima Zahara (as) me yafi kyawunta daga maganar komaini (rd) fadinsa: lallai da ace a bayan annabi akwai wani annabi da zai zo da Fadima zata kasance, lallai yadda al'amarin yake shi ne ishara ce zuwa wannan ma'ana, kamar yadda wani mawaki ke cewa: ita Fadima itace Ahmadu na biyu.

Idan wani mutum cikin bayaninsa ya bayyana wani mutum da misalin wannan jumla: lallai shi tsoka ce daga gare ni, hasken idona, farin cikin zuciyata, ruhina wanda ke tsakanin geffana….. lallai daga adadin wadannan siffofin da hikayoyi zamu fitar da natija da sakamako da cewa lallai wancan mutumin lallaishi yana daga samuwarsa kebantatta, kamar yadda ya zo cikin hadisin bargo (su daga gare ni suke nima daga gare su nake) ya kuma fadinsa: (yana mini radadi dukkanin abin dayake musu radadi sannan dukkanin abin dayake faranta musu yana faranta mini)

Fakrul Razi limamin masu shakka yana cewa: cikin tafsirin ayatul tadhiri: lallai Ahlil-baiti suna cikin siffofi biyar, daga cikin su: tsarkaka, annabi shi tsarkakakke ne kamar yadda ya zo cikin fadinsa madaukaki  

(طه * مَا أنْزَلْنَا عَلَيْکَ القُرْآنَ لِتَشْقَى ) ،

Daha*bamu saukar maka da kur'ani ba don kasha wahala.[1]

Ma'ana ya tsarkakakke, hakama Ahlil-baiti suna tarayya ciki suna daidaita da annabi cikin tsarkakarsa da tsaftarsa da ismarsa.



[1] Taha:1