sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
  • MAULIDIN IMAM HASSAN ASKARI
  • SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI CIGABA DA BAHASUL KARIJ
  • MUNA MIKA TA’AZIYA GA DAUKACIN GURGUZUN AL’UMMAR MUSULMI BISA SHAHADAR IMAM ALIYU IBN MUSA ARRIDA (A.S)
  • TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH DA DANSA IMAM HASSAN (A.S
  • SABUWAR SHEKARAR MUSLUNCI 1441 TARE DA DAWOWA KARATU DAGA RANAR ASABAR 14 GA WATAN MUHARRAM
  • BAYANI DANGANE DA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAM SHEKARA TA 1441 H
  • BAYANI KAN MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAHAM SHEKARA 1441 H KASHI NA (2)
  • BAYANI NA FARKO (1) BISA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAMAN SHEKARA 1441 H
  • TASHAR KARBALA IRFAN ZASU WATSA LACCOCIN ASHURA NA SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI
  • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Suldanul Nufus Aliyu bn Musa Arrida (as)
  • Makalar Hubbun Nisa’i fi Hadisun Nabawi ta fito- tare da Alkamalin Assayid Adil-Alawi
  • Makalar Annaji Bashar Mau’udul Muntazar ta fito tareda Alkalamin Assayid Adi
  • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Jafar bn Muhammad
  • Makalar duba li mushatulArba’in tareda Alkalamin Assayid Adil-Alaw
  • Allah ya girmama ladan ku da na mu bisa musibar rashin Sarkin muminai Ali (as)
  • Tunawa da Ranar haihuwar Imam Aliyu bn Husaini Zainul Abidin Amincin Allah ya tabbata a gare shi
  • Maulidin Abul Fadlul Abbas bn Ali (as) and akewa lakabi da Kamaru Banu Hashim mai shayar masu kishi a Karbala
  • Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Jawad (as)
  • Ranar asabar 14 ga watan Rabi’u Awwal Assayid Adil-Alawi (h) zai cigaba da bada darasin bahasul karij
  • muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar da aka haifi Imam Hassan Askari (as)
  • Labarai wanda akafi karantawa

    Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Jawad (as)

    Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Jawad (as)

    Kissar haihuwarsa amincin Allah ya kara tabbata a gareshi:

    Sayyada Hakima `yar Imam Kazim (as) ta rawaito yanda aka haife shi  mai girman daraja da karamomin da suka bayyana, sai take cewa:

    لمّا حضرت ولادة خيزران أُمّ أبي جعفر(عليه السلام)، دعاني الرضا(عليه السلام) فقال: «يا حكيمة، اِحضَري ولادتها

    وأدخلني(عليه السلام) وإيّاها والقابلة بيتاً، ووضع لنا مصباحاً، وأغلق الباب علينا.

    فلمّا أخذها الطلق طَفئَ المصباحُ، وبين يديها طست فاغتممتُ بطفي المصباح، فبينا نحن كذلك إذ بدر أبو جعفر(عليه السلام) في الطست، وإذا عليه شيء رقيق كهيئة الثوب، يسطع نوره حتّى أضاء البيت فأبصرناه.

    فأخذتُه فوضعتُه في حِجري، ونزعتُ عنه ذلك الغشاء، فجاء الرضا(عليه السلام) ففتح الباب، وقد فرغنا من أمره، فأخذه(عليه السلام) ووضعه في المهد وقال لي: «يا حكيمة، الزمي مهده».

    قالت: فلمّا كان في اليوم الثالث رفع(عليه السلام) بصره إلى السماء، ثمّ نظر يمينه ويساره، ثمّ قال(عليه السلام): «أشهدُ أن لا إِلَه إلّا الله، وأشهدُ أنّ مُحمّداً رسولُ الله».

    فقمتُ ذعرة فزِعةً، فأتيتُ أبا الحسن(عليه السلام) فقلت له: سمعتُ من هذا الصبي عجباً؟! فقال(عليه السلام): «وما ذاك»؟ فأخبرته الخبر، فقال(عليه السلام): «يا حكيمة، ما تَرَونَ مِنْ عجائبه أكثر

    Lokacin da nakuda ta kama Kizaran mahaifiyar Imam Jawad (as) sai Imam Rida (as) ya kirani yace: ya Hakima ki shirya karbar haihuwarta, sai Imam (as) ya shiga da ni daki tareda unguwar zoman da zata karbi haihuwar ya bamu fitila ya kulle kofa, lokacin da  na kuda ta tsananta kanta sai fitilar ta mutu, a gabata akwai wata yar kwarya sai ta suma sakamakon mutuwar wannan fitila, yayin da muke cikin wannan hali sai ga hasken Abu Jafar Jawad cikin wannan kwarya, sai muka ga wani siririn abu kan jikinsa kamar tufafi, hasken na ta huda har sai da ya haskaka dakin muka ganshi, sai Imam Rida (as) dauke shi ya dora shi kan shimfida yace: ya hakima ki lazimci makwancinsa, Hakima tace: rana ta uku da haihuwarsa sai Imam Jawad (as) ya daga kansa sama ya dubi damansa da hagunsa sannan yace: na shaida babu abin bauatawa da gaskiya sai Allah Muhammad manzonsa ne sai kawai na tashi a firgice cikin tsoro na tafi wajen Imam Rida (as) nace masa na ji wani abin ban mamaki daga wannan jinjiri?! Sai yace: me kika ji? Sai na bashi labari, sai yace: ya Hakima kadan kika gani daga abubuwan ban mamakinsa.

    Daga wasiyoyinsa (as)

    ۱ـ قال(عليه السلام): «العَامِل بالظلمِ، والمُعينُ عليهِ، والراضِي به شُرَكَاءٌ

    Amincin Allah ya tabbata a gareshi yana cewa: mai aiki da zalunci da mai taimakonsa kai, da wanda ya yarda dukkansu abokanan tarayya ne.

    ۲ـ قال(عليه السلام): «أربعُ خِصالٍ تُعيِّنِ المَرءَ على العمل: الصحّة، والغِنَى، والعِلم، والتوفِيق

    Aminci Allah ya kara tabbata a gareshi yace: abubuwa guda hudu suna taimakon mutum kan aiki: lafiya, wadata, ilimi, taufiki.

    ۳ـ قال(عليه السلام): «إنّ لله عباداً يخصّهم بالنعم ويقرّها فيهم ما بذلوها، فإذا منعوها نزعها عنهم وحوّلها إلى غيرهم

    Amincin Allah ya kara tabbata a gareshi yace: Allah yana da wasu bayi da yake kebantarsu da ni’imomi yake ku tabbatar da su cikin matukar sun sadaukar da su, idan suka noke suka hana sai Allah ya zare wadannan ni’imomi daga garesu ya mika su ga wasunsu.  

    ۴ـ قال(عليه السلام): «من استغنى بالله افتقر الناس إليه، ومن اتّقى الله أحبّه الناس وأن كرهوا

    Amincin Allah ya tabbata a gareshi yace: duk wanda ya wadatu da Allah mutane zasu bukatu zuwa gareshi, duk wanda yaji tsoran Allah mutane zasu so shi ko basa so.

    ۵ـ قال(عليه السلام): «لن يستكمل العبد حقيقة الإيمان حتّى يؤثر دينه على شهوته، ولن يهلك حتّى يؤثر شهوته على دينه

     Amincin Allah ya tabbata a gareshi: bawa bai cika hakikanin Imani har sai ya fifita addininsa kan sha’awarsa, kuma bawa bazai taba halaka har ya fifita sha’awarsa kan addininsa.

    ۶ـ قال(عليه السلام): «الفضائل أربعة أجناس: أحدها الحكمة وقوامها في الفكرة، والثاني العفة، وقوامها في الشهوة، والثالث القوّة وقوامها في الغضب، والرابع العدل وقوامه في اعتدال قوى النفس»

    Amincin Allah ya tabbata a gareshi yace: faloli jinsi hudu ne: na farkonsu hikimad da daidaitarta cikin tunani, na biyu kame kai daga biyewa sha’awa, tsayuwarsa na cikin sha’awa, na uku karfi tsayuwarsa na cikin fushi, na hudu adalci tsayuwarsa na cikin daidaita karfin nafsu.