sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
  • MAULIDIN IMAM HASSAN ASKARI
  • SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI CIGABA DA BAHASUL KARIJ
  • MUNA MIKA TA’AZIYA GA DAUKACIN GURGUZUN AL’UMMAR MUSULMI BISA SHAHADAR IMAM ALIYU IBN MUSA ARRIDA (A.S)
  • TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH DA DANSA IMAM HASSAN (A.S
  • SABUWAR SHEKARAR MUSLUNCI 1441 TARE DA DAWOWA KARATU DAGA RANAR ASABAR 14 GA WATAN MUHARRAM
  • BAYANI DANGANE DA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAM SHEKARA TA 1441 H
  • BAYANI KAN MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAHAM SHEKARA 1441 H KASHI NA (2)
  • BAYANI NA FARKO (1) BISA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAMAN SHEKARA 1441 H
  • TASHAR KARBALA IRFAN ZASU WATSA LACCOCIN ASHURA NA SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI
  • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Suldanul Nufus Aliyu bn Musa Arrida (as)
  • Makalar Hubbun Nisa’i fi Hadisun Nabawi ta fito- tare da Alkamalin Assayid Adil-Alawi
  • Makalar Annaji Bashar Mau’udul Muntazar ta fito tareda Alkalamin Assayid Adi
  • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Jafar bn Muhammad
  • Makalar duba li mushatulArba’in tareda Alkalamin Assayid Adil-Alaw
  • Allah ya girmama ladan ku da na mu bisa musibar rashin Sarkin muminai Ali (as)
  • Tunawa da Ranar haihuwar Imam Aliyu bn Husaini Zainul Abidin Amincin Allah ya tabbata a gare shi
  • Maulidin Abul Fadlul Abbas bn Ali (as) and akewa lakabi da Kamaru Banu Hashim mai shayar masu kishi a Karbala
  • Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Jawad (as)
  • Ranar asabar 14 ga watan Rabi’u Awwal Assayid Adil-Alawi (h) zai cigaba da bada darasin bahasul karij
  • muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar da aka haifi Imam Hassan Askari (as)
  • Labarai wanda akafi karantawa

    Wasika ta uku ta karshe dangane da ra’ayoyin sayyid Kamalul haidari

     

    Wasika ta uku ta karshe dangane da ra’ayoyin sayyid Kamalul haidari

    Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

     

     

    Ya ubangijina ka buda bakina da shiriya kai mini ilhama da takawa

    ﴿اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ﴾.

    Ka shiryar damu tafarki madaidaici.

    Yan’uwana maza da mata masoyana salamu Alaikum, Allah ya dawwamar daku cikin alheri da taufiki da dandagatar da kyakkyawan karshe,

    Wannan itace wasikata ta uku kuma ta karshe dangane da wanda ya tsunduma ni ta hanyar tambayar da yayi mini dangane da minhajiyar sayyid Kamalul haidari, zan fadi karara da bayyanarwa da gaskiya muna rokon Allah sabati ga kowa da kowa kan wilayar sarkin muminai da iyalansa tsarkaka da wanzuwa cikin inuwar kur’ani da sahibul Asri waz’zaman Allah ya gaggauta bayyanarsa madaukakiya, lallai wilaya Alawiyya nabawiyya ita ce tafarki madaidaici siradi mikakke Allah ya azurtamu baki daya da kyakkywan karshe.

    Da farko: ban kasance ina nufin suka da ishkali kan tsarin tafiyar Kamalul haidari da ra’ayoyinsa  cikin wasika ta farko da ta biyu da wannan ta karshe ba, kadai dai na nufin baiwa mai tambaya labari atakaice da yanayi na gama gari da cewa lallai shi Akaramakallahu sayyid Kamnalul a yanzu fa yanada wasu bakin ra’ayoyi da suka ratse suka sabawa abinda jamhur din manya-manyan malamanmu suka tafi akai daga hauzar Najaful Ashraf da birnin qum mai tsarki, wannan ra’ayoyin nasa sun ratse daga abinda hauza ilimiya take tafiya kai da abinda magabata nagari suka tafi kai dama wanda suka zo bayansu cikin bahasosinsa da sabuwar minhajarsa, wannan wani abune wand akowa ya sani babu banbanci daga mai sabani da mai laminta, amsata ga mai tambaye ta kasance daga fuskacin bada labari daga cikin gida zuw awaje bawai kan hakikanin abun ba daga babin bayanin bayyanannun abubuwa na fili, sai dai cewa a zahiri ba’arin daga wasu yan’uwa sun karanta amsa tareda abinda ke cikin kwakwalensu daga natijar abubuwan da suka ginu kai da suka gabata daga wanda suka dace da kuma wanda suke da sabani, saboda haka wannan matsala ba daga gareni take ba kadai tana daga wasu adadi matakai nasu kansa, kamar yadda ake cewa: me yasa kake baka sukansa a ilimance ka kawo wasu maudu’ai da ishkaloli da shubuhohi  maimakon bada amsa da amsa ta gama gari? to anan da farko sai ince: azurtacce shine wand aya wadatu da waninsam hakika wasu ba’ari sun daukar ma kansu sukansa da kalubalantarsa daga cikinsu akwai wanda yayi rubuta aka buga daga cikinsu kuma akwai wanda ya bi irin wannan hanyar da na bi.

    Hakika mahaifina tun farko-farkon fara karatuna a hauza yayi mini ladabi da cewa in gayawa mutane kyakkyawar magana, kuma inyi kira zuwa garenbi daga daddadan nono- wannan daga babin misali kenan, kuma kada in dinga suka kan nonon da yake wurin wasu da fadin cewa tsami gareshi, lallai mutane masu hankali da kansu zasu dandana su banbance zazzakan nono daga tsatstsama Allah ne mai datarwa da damdagatar.

    Sannan ya zo cikin ma’anar wani hadisi da cewa             

     (العاقل من يضع الأشياء في مواضعها)

    Shi mai hankali shine mai ajiye abubuwa a muhallansu.

    babu shakka cewa shi sayyid yana daga cikin ma’abota hankali masu daraja, sai dai cewa shi kamar yadda ta bayyanar mini (iliminsa ya zarce hankalinsa) amma ba da ma’anar nakasta shi ba, kada Allah ya tauye masa hankali, bari dai abinda ya dace gareshi shine ya ajiye iliminsa a muhallin da ya dace da shi, ya bijiro da abind ayake wurinsa daga sabo cikin bahasosi, kan fadin abokansa daga sabunta zamani da ilimi cikin nutsuwa da rusunawa, cikin girma da kyawu da yanayi da yafi dacewa ba tareda raunana hauza da yan hauza daga malamai magabata da na zamani, bari dai da dukkanin iklasi da bin tsarin hankali tareda neman taimakon Allah da kyakkyawa mai tajalli cikin taimakon hauzozi da maraji’ai da malaman addini daga wadanda suke takaicin abinda yake aikatawa, ba a gushe ba ana takaici da bakin cikin rashin mutum irinsa ba, bari daga cikinmu akwai wadanda har yanzu suke fatan kasantuwarsa nan gaba ya zama makoma mai haske da amfani ga addini da mazhaba  da hauzozin ilimi  da jama’a da dukkanin mutane sosai-sosai, babu tsimi babu dabara sai ga Allah madaukaki mai girma.

    Ku sani hakika gabanin shekara guda mun hadu da shi mun gaisa, hakika gabanin shekara mun kasance tareda shi da dana da ma’abocin gida kan walimar abincin isha’i kan gayyatar ma’abocin gidan bisa munasabar bikin dan mai gidan wanda ya kasance daga daliban hauza, sannan zamanmu ya tsawaita fiye da awa biyu mun kuma kasan ce muna tattaunawa da juna kan batutuwa daban-daban daga abind aya ta’allaka da ra’ayoyinsa kebantattu mun yi tattaunawar cikin barkwanci na ilimi  cikin nutsuwa da nishadi, lokacin da zamu yi sallama da bankwana muka rungumi juna kowanne na girmama juna ba tareda sukan juna ba, sai dai fa hakan bai nufin in bye masa in yarda da dukkanin ra’ayoyinsa in tafi kan abind aya tafi kai, lallai shi yanada ra’ayoyi daga cikinsu akwai karbabbu kyawawa hakama akwai ababen watsi da tattaunawa kansu da bahasi, sai dai cewa yana bayyanar mini Allah ne masani abinda ya bijirar daga ratsatstsan bahasi da ra’ayi daga gareshi ba zai zaunu ba nan gaba daga abinda yake fafutikarsa na habbaka hauza ilimiya  da gyaranta kamar yadda yake fadi, har muslunci da shi’anci ya wayi gari karbabbe wurin wayayyun mutane daga samari yan jami’a , lallai yadda al’amarin yake shine ra’ayoyinsa na karshe-karshe basu samu karbuwa ba hatta wurin kusoshin hauza jigajiganta, to me kake tsammani kuma nan gaba kadai dai babu mai karbar wadannan ra’ayoyi nasa sai wadanda suke kan hanyar irin tasa, lallai dacewa da juna dalili ne na hadewa dda juna.

    Daga karshe ma ta kai ga hatta tashoshi tauraronb dan adam na shi’a sun fara watsi da shi. Kamar yadda ta kasance a baya. Kai hatta tashar Alkausar wacce da ta kasance kasuwar bajakolin ra’ayoyinsa da tunaninsa suma sunyi watsi da shi sun ki yadda ya cigaba da bajokolin ra’ayoyinsa, lallai ni nasan abubuwan da baku sani ba babu tsimi babu dabara sai ga Allah madaukaki mai girma.

    Daga cikin abin ban nishadi da dariya a wancan dare a muka hadu gidan wancan mutumi, bayan mun zauna mun gama lale da maraba da juna sai wannan mai gida Allah ya dawwamar da daukakarsa yace: lallai ni lokacin da naje hajji wasu ba’arin mahajjata da sayyid Kamalul haidari ya kasance yana birge su sun dinga tambayata gameda shi, sai cikin murmushi nace wannan ya kasance shekara nawa kenan ? sai yace: gabanin shekaru shida da suka shude suka wuce, sai sayyid Kamalul haidari ya daga murya yace: (shin wai ko ka fahimci manufar tambayar sayyid Adil Alawi? Yana son yace kadai dai hakan ya kasance a lokacin da nake kan shiriya sai dai cewa a yau......) sai muka fashe da dariya wannan shine sababin budewar kofar tattaunawa tareda sayyid muka gama tattaunawar har zuwa lokacin da sayyid kamalul haidari yake cewa: kamar yadda sayyid sistani (dm) yake d ara’ayi nima inada ra’ayina na kaina, kuna da ra’ayinku nima inada ra’yina, sai na ce masa yayi kyau mu zuba ido muga mai zai kasance nan gaba ga wanene fage zai kasance da lokaci, Allah ne mai bada kariya shine majibanci.

    Sannan dana sayyid Muhammad Alawi Ya rubuta makala da alkalaminsa mai shafi 20 sai dai har zuwa yanzu lokaci yada ta bai yi sakamakon wasu yanayiyyika ta yiwu a yada ta nan gaba domin fa’idantuwa da izinin Allah.

    Abu na  karshe: daga wannan mimbari na gidan annabta ina aika gaisuta ga sayyid ina yi masa addu’a da kuma kaina da dukkanin mutane da shiriya da kyakkyawan karshe     

     

    (إهدنا الصراط المستقيم صراط الذين أنعمت عليهم)

    Ka shiryar damu tafarki madaidaici tafarkin wadanda kai ni’ima kansu.

    Daga annabawa da siddikai da salihai wadannan sun kyautata zama abokan tafiya,

    Lallai ni na sauke nauyi na yafe daga wanda yaci nama ya soke da konannen harshe, sabod ayana jahilta ta yana kuma jahiltar abinda na nufa daga wasikuna lallai shi ya samu uzuri, sai dai cewa kuji tsoran Allah hakikanin tsoransa, kuji tsoran Allah cikin maraji’ai da malamai da hauzozi, amincin Allah ya tabbata gareku, karshen maganarmu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai

    18 jimada sani 1439