sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
  • MAULIDIN IMAM HASSAN ASKARI
  • SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI CIGABA DA BAHASUL KARIJ
  • MUNA MIKA TA’AZIYA GA DAUKACIN GURGUZUN AL’UMMAR MUSULMI BISA SHAHADAR IMAM ALIYU IBN MUSA ARRIDA (A.S)
  • TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH DA DANSA IMAM HASSAN (A.S
  • SABUWAR SHEKARAR MUSLUNCI 1441 TARE DA DAWOWA KARATU DAGA RANAR ASABAR 14 GA WATAN MUHARRAM
  • BAYANI DANGANE DA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAM SHEKARA TA 1441 H
  • BAYANI KAN MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAHAM SHEKARA 1441 H KASHI NA (2)
  • BAYANI NA FARKO (1) BISA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAMAN SHEKARA 1441 H
  • TASHAR KARBALA IRFAN ZASU WATSA LACCOCIN ASHURA NA SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI
  • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Suldanul Nufus Aliyu bn Musa Arrida (as)
  • Makalar Hubbun Nisa’i fi Hadisun Nabawi ta fito- tare da Alkamalin Assayid Adil-Alawi
  • Makalar Annaji Bashar Mau’udul Muntazar ta fito tareda Alkalamin Assayid Adi
  • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Jafar bn Muhammad
  • Makalar duba li mushatulArba’in tareda Alkalamin Assayid Adil-Alaw
  • Allah ya girmama ladan ku da na mu bisa musibar rashin Sarkin muminai Ali (as)
  • Tunawa da Ranar haihuwar Imam Aliyu bn Husaini Zainul Abidin Amincin Allah ya tabbata a gare shi
  • Maulidin Abul Fadlul Abbas bn Ali (as) and akewa lakabi da Kamaru Banu Hashim mai shayar masu kishi a Karbala
  • Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Jawad (as)
  • Ranar asabar 14 ga watan Rabi’u Awwal Assayid Adil-Alawi (h) zai cigaba da bada darasin bahasul karij
  • muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar da aka haifi Imam Hassan Askari (as)
  • Labarun da ba tsammani

    Labarai wanda akafi karantawa

    MAULIDIN IMAM HASSAN ASKARI

     

    Allah ya faranta kwanakinku bisa munasabar zagayowar ranar haihuwar Imam Hassan Askari amincin Allah ya kara tabbata a gareshi.

    Daga zantukansa amincin Allah ya kara tabbata a gareshi:

    «لا يعرف النعمة إلّا شاكر، ولا يشكر النعمة إلّا العارف ».

    Babu wanda ya san darajar ni’ima sai mai yin godiya kanta, babu mai nuna godiya kan ni’ima sai Arifi wanda ya san ni’imar.

    «من الذنوب التي لا تغفر: ليتني لا اُؤاخذ إلّا بهذا».

    Daga cikin zunaban da ba a gafarta su: fadin inama dai nib a zan a tuhume ni da komai sai wannan laifin.

    «من مدح غير المستحقّ للمدح فقد قام مقام المتّهم ».

    duk wanda ya yabi wanda bai cancanci yabo ba hakika ya tsaya matsayar abin tuhuma.

    «من رضي بدون الشرف من المجلس لم يزل الله وملائكته يصلّون عليه حتّى يقوم

    Duk wanda ya hakura ya yarda da Kankan da kai daga majalisi Allah da Mala’iku ba zasu gushe ba suna yi masa addu’a har sai ya tashi daga wajen.

    «جعلت الخبائث في بيت ، وجعل مفتاحه الكذب ».

    An sanya dukkanin munanan ayyuka cikin wani gida, sannan an sanya karya a matsayin makullin wannan gida.

    «حسن الصورة جمال ظاهر، وحسن العقل جمال الباطن ».

    Kyawuntar sura shine kyawun zahiri, kyawuntar hankali shine kyawun badini.

    «إعلم أنّ للحياء مقدارآ، فإن زاد على ذلک فهو ضعف ، وللجود مقدارآ فإن زاد على ذلک فهو سرف ، وللاقتصاد مقدارآ فإن زاد عليه فهو بخل ، وللشجاعة مقدارآ فإن زاد فهو التهوّر».

    Ka sani kunya tana iyaka idan ta shallake shi sai ta zama rauni, ka sani kyauta tana haddi idan ta shallake haddinta sai ta zama barna, ka sani tattali yana da iyaka idan ya shallake wannan iyaka sai ya zama rowa, jarumta tana haddi idan ta shallake shi sai ta zama rashin hankali.

    «لا تمارِ فيذهب بهاؤک ، ولا تمازح فيجترأ عليک ».

    Ka da ka dinga yin jayayya sai kwarjininka ya zube, kada kayi barkwanci sai a samu damar yi maka rashin kunya da tsageranci.

    «آخر ما يخرج من قلوب الصدّيقين حبّ الرئاسة ».

    Karshen abinda zai fita daga zukatan Siddikai shine son shugabanci.

    «من استأنس بالله استوحش من الناس ».

    Duk wanda ya samu nutsuwa da Allah sai ji rasa nutsuwa da mutane.

    Ya cewa shi’arsa:

    «اُوصيكم بتقوى الله، والورع في دينكم ، والاجتهاد لله، وصدق الحديث ، وأداء الأمانة إلى من ائتمنكم من برٍّ أو فاجر، وطول السجود، وحسن الجوار، فبهذا جاء محمّد  6».

    Ina yi muku wasicci da tsoran Allah da tsantseni cikin addininku da zage dantse domin Allah, da gaskiyar zance, da sauke amana ya zuwa wanda ya baku ajiyar amana daga mutumun kirki da fajiri, da tsawaita sujjada, da kyawunta makotaka, da wannan ne Muhammad (s.a.w) ya zo da shi.

    «صلّوا في عشائرهم ، واشهدوا جنائزهم ، وعودوا مرضاهم ، وأدّوا حقوقهم ، فإنّ الرجل منكم إذا ورع في دينه ، وصدق في حديثه ، وأدّى الأمانة ، وحسن خلقه مع الناس ، أي مع مطلق وعموم الناس ، قيل هذا شيعي ، فيسرّني ذلک ، فاتّقوا الله وكونوا زينآ، ولا تكونوا شينآ، جرّوا إلينا كلّ مودّة ، وادفعوا عنّا كلّ قبيح ، فإنّه ما قيل فينا من حسن فنحن أهله ، وما قيل من سوء فما نحن كذلک ، لنا حقّ في كتاب الله وقرابة من رسول الله وتطهير من الله.

    Ku yi sallah cikin mutanensu, ku halarci jana’izarsu, ku ziyarci marasa lafiyarsu, ku sauke hakkokinsu, lallai mutum daga cikinku idan yayi taka tsantsan cikin addininsa, yay a fadi gaskiya cikin zancensa, ya sauke amana, ya kyautata dabi’arsa tareda mutane (tareda dukkanin mutane) aka a ce wannan dan shi’ata ne, lallai haka yana faranta mini, kuji tsoran Allah ku kasance ado ka da ku kasance aibu, ku jawo mana dukkanin kauna, ku tunkude mana dukkanin mummuna, lallai abinda aka fadi cikinmu daga kyawu lallai mu ahalinsa ne, abinda aka fadi daga mummuna cikinmu mu bamu kasance ahalinsa ba, muna da hakki cikin littafin Allah da kusanci daga Manzon Allah da tsarkaka daga Allah.

    «من التواضع السلام على كلّ من تمرّ به ، والجلوس دون شرف المجلس ».

    Daga tawali’u akwai yin sallama kan duk wand aka wuce ta gefansa da zama gefan majalisi.

    «حبّ الأبرار للأبرار ثواب للأبرار، وحبّ الفجّار للأبرار فضيلة للأبرار، وبغض الفجّار للأبرار زين للأبرار، وبغض الأبرار للفجّار خزيٌ على الفجّار».

    Soyayyar Rabautattu ga Rabautattu lada ce ga rabautattu, soyayyar Fajirai ga Rabautattu falala ce ga rabautattu, kiyayyar fajirai ga rabautattu ado ce ga Rabautattum kiyayyar Rabautattu ga Fajirai tozarta ce ga Fajirai

    «ليست العبادة كثرة الصيام والصلاة ، وإنّما العبادة كثرة التفكّر في أمر الله».

    Ibada ba shine yawan azumi da sallah ba, kadai dai ibada shine yawan tunani cikin lamarin Allah

    «بئس العبد عبدٌ يكون ذا وجهين وذا لسانين ، يطري أخاه شاهدآ ويأكله غائبآ، إن اُعطي حسده ، وإن ابتلي خانه ».

    Tir da bawan da yake kasancewa ma’abocin fuska biyu da harshe biyu yana yabon dan’uwansa idan yana kusa da shi yana cin namansa da yin tseguminsa ind aya faku, idan aka yi masa kyauta sai yayi masa hassada, idan ya shiga cikin jarrabawa sai ya ha’ince shi.

    الغضب مفتاح كلّ شرّ».

    Fushi shine makullin dukkanin sharri.

    «أقلّ الناس راحةً الحقود».

    Mafi karancin hutu cikin mutane shine mai kulli a cikin zuciyarsa da gaba da wani

    «خصلتان ليس فوقهما شيء: الإيمان بالله ونفع الإخوان ».

    Abubuwa guda biyu babu wani abu da yake samansu: Imani da Allah da amfanar da yan’uwa.

    «جرأة الولد على والده في صغره تدعو إلى العقوق في كبره ».

    Tsageranci da yaro yake yiwa mahaifinsa a lokacin yarintarsa tana jawo sabawa iyaye a lokacin girmansa.

    «ليس من الأدب إظهار الفرح عند المحزون ».

    Baya daga cikin ladabi bayyana farinciki a wurin wanda yake cikin bakin ciki.