sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
  • MAULIDIN IMAM HASSAN ASKARI
  • SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI CIGABA DA BAHASUL KARIJ
  • MUNA MIKA TA’AZIYA GA DAUKACIN GURGUZUN AL’UMMAR MUSULMI BISA SHAHADAR IMAM ALIYU IBN MUSA ARRIDA (A.S)
  • TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH DA DANSA IMAM HASSAN (A.S
  • SABUWAR SHEKARAR MUSLUNCI 1441 TARE DA DAWOWA KARATU DAGA RANAR ASABAR 14 GA WATAN MUHARRAM
  • BAYANI DANGANE DA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAM SHEKARA TA 1441 H
  • BAYANI KAN MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAHAM SHEKARA 1441 H KASHI NA (2)
  • BAYANI NA FARKO (1) BISA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAMAN SHEKARA 1441 H
  • TASHAR KARBALA IRFAN ZASU WATSA LACCOCIN ASHURA NA SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI
  • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Suldanul Nufus Aliyu bn Musa Arrida (as)
  • Makalar Hubbun Nisa’i fi Hadisun Nabawi ta fito- tare da Alkamalin Assayid Adil-Alawi
  • Makalar Annaji Bashar Mau’udul Muntazar ta fito tareda Alkalamin Assayid Adi
  • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Jafar bn Muhammad
  • Makalar duba li mushatulArba’in tareda Alkalamin Assayid Adil-Alaw
  • Allah ya girmama ladan ku da na mu bisa musibar rashin Sarkin muminai Ali (as)
  • Tunawa da Ranar haihuwar Imam Aliyu bn Husaini Zainul Abidin Amincin Allah ya tabbata a gare shi
  • Maulidin Abul Fadlul Abbas bn Ali (as) and akewa lakabi da Kamaru Banu Hashim mai shayar masu kishi a Karbala
  • Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Jawad (as)
  • Ranar asabar 14 ga watan Rabi’u Awwal Assayid Adil-Alawi (h) zai cigaba da bada darasin bahasul karij
  • muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar da aka haifi Imam Hassan Askari (as)
  • Labarun da ba tsammani

    Labarai wanda akafi karantawa

    BAYANI NA FARKO (1) BISA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAMAN SHEKARA 1441 H

     

    Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

    Amincin Allah ya tabbata a gareku yaku taron muminai masoya Imam Husaini (as)

    Bayan haka:

    Hakika Allah mai hikima cikin littafinsa mai girma yana cewa:

     ﴿وَمَنْ يُعَظِّمْ شَعَائِرَ اللَّهِ فَإِنَّهَا مِنْ تَقْوَى الْقُلُوبِ

    Duk wanda ya girmama ibadojin Allah lallai yana daga takawar zukata.

    Babu kokwanto cewa mu `yan shi’a imamiya masu wilaya da soyayyar Ahlil-baiti A’imma Ma’asumai amincin Allah ya kara tabbata a garesu kuma daga mabiya mazhabarsu cikin akida da aiki, lallai muna Imani muna rayawa sakamakon abin da yake a hannun mu daga dalilai da hujjoji, da kuma umarnin imamanmu tsarkaka amincin Allah ya tabbata a garesu da cewa lallai cikin zamanin Gaiba Kubra cikin inganta ayyukanmu na addini da na fikihu daga ibada da mu’amala, kadai dai cikinsu muna komawa zuwa ga Malaman fikihu masu girman daraja da duk wanda ya kasance ya cika sharudda cikin mukamin bada fatawa, lallai duk wani Mukallafi dole dai ya kasance daya daga cikin mutane uku: ko dai ya kasance masani fikhu da zai iya ciro hukunce-hukuncen shari’a daga dalilanta na filla-filla daga littafin Allah da sunna da Ijma’I da Aklu, sai ya kasance Fakihi daga cikin wadanda suka goge suka samu kwarewa a wannan fanni, ko kuma dai ya kasance Mukalladi sai ya koma zuwa ga masana fannin da ciro hukunci, kamar yanda lamarin yake cikin dukkanin fannoni da ilimi, hakan na kasance cikin babin komawar wanda bai da sani zuwa ga wanda yake da sani, wannan shi ne abin da dalilin hankali ya ginu a kai dama dalilin nakali daga littafi da sunna, kamar yanda dailin wujdani da Zauki da Irfani daga kashafi da shuhudi suka tafi akai, ko kuma dai ya kasance Muhtadi sai kasance tsakatsaki tsakanin Ijtihadi da Taklidi, hakan na tabbatuwa idna ya kasance daga Ahalin ilimi da daraja ya kuma san wurare da muhallan da ake yin ihtiyadin, a cikin siyakin da korowar wannan asali daga Ijtihadi da taklidi  da ihtiyadi ya zama wajibi a kanmu a dokance da hankalce da shari’ance mu gangaro da ayyukanmu na ibada kamar sallah wacce ta kasance ginshikin addini haka mu’amaloli kamar misalin kasuwanci mu kai su zuwa ga masana wannan fanni cikin fikhu da fakihanci, a kan hasken wannan al’amari na kullawa da aiki ya zama wajibi dukkanin ibadojin bukukuwan raya zaman makokin Ashura wadanda suka kasance daga tajallin ibadojin Allah tantattu da akai musu dabaibayi da dabaibayi guda biyu: dacewa da hankali da shari’a, lallai addinin muslunci wanda shi addinin Imam Husaini (as) kuma addinin Muhammad a samance da Husaini cikin wanzuwars, hakika yunkurin Imam Husaini (as) da gwagwarmayarsa  da shahadarsa tsarkakka, ko dai ta kasance dacacciyar da hankali cikin farar da ita kamar yanda take tare da shari’a a samance da wanzuwa, lallai tana daga wahayin da ya zo daga sama

    (شاء الله أن يراك قتيلاً)

    Allah ya so ya ganka a kashe.

    A wannan lokaci ya zama dole dukkanin wata ibada daga tsarkakkun ibadoji babu banbanci cikin kasantuwarsu na da can na zamanin da ya shude ko kuma sababbi ko kuma daga wadanda ake sabunta su bisa sassabawa zamani da wurare bisa la’akari da masu raya ta’aziyar da bukukun zaman juyayi ya zama dole su kasance karkashin dokoki da hukuncin Allah domin aikin ibadar ya samu ingantuwa, sannan ya zama karbabbe a samu lada kan aikata shi, idan ko ba haka ba to fa lallai wajibi mu sani al’amarin Husaini (as) da yunkurinsa mai albarka bai kasance sama da kur’ani mai girma ba, lallai hadisi ya zo daga Manzon Allah (s.a.w)

     (رُبّ تالٍ للقرآن والقرآن يلعنه).

    Sau da yawa zaka samu mutum yana karanta kur’ani kuma kur’ani yana la’antarsa.

    Idan tilawarsa ta kasance ta sabawa abin da kur’anin yake umarni da shi, ya kuma kasance baya zartar da abin da yake kunshe cikinsa, baya tsayar da haddodinsa.

    Haka al’amarin yake cikin al’amarin Mimbarorin Husaini (as) da dukkanin masu hawa samansu daga masu Huduba da Mawaka da masu karanta ta’aziyar shugaban shahidai (as) sau da yawa zaka samu mai karanta huduba ga Imam Husaini (as) amma kuma shi Imam din yana tsine masa, haka nawa ne daga masu wake ga Imam amma kuma Imam (as) yana tsine musu, nawa da daga mai raira ta’aziya da masu hidima cikin maukibin Imam Husaini (as) amma kuma yana tsine, hakan na gudana cikin dukkanin ibadojin Ashura da masu raya su, cikin karami da babba, wajibi ibadarka ga raya lamarin Husaini (as) ta kasance cikin dabaibayin shari’a tsarkakka, sannan cikin dukkanin mai son zuwa da sabon abu wajbi kansa ya nemi fatawa daga wurin Maraji’ai masu daraja, da wadanda suka kasance sun cika sharuddan fatawa, wandanda suka kasance masu katange kawukansu masu sabawa son rai, masu biyayya ga ubangiji cikin ake zabar wanda za a yiwa taklidi  cikin sallah da azumi da hajji daga wurinsa ne zaka karbi fatawa cikin jihadinka kan haka idan aka kasheka zaka kasance shahidi

     ﴿أَحْيَاءٌ عِنْدَ رَبِّهِمْ يُرْزَقُونَ﴾.

    Rayayyu ne suna azurtuwa wurin ubangijinsu.

    Hakan lamarin yake cikin tsayar da ibadojin Husaini (as), lallai basu kasance wajen dokokin Allah ba, basu kasance saman sallah wacce take ginshikin addini ba, wacce idan ta karbu sai sauran ayyuka su karbu, idan kuma akai wurgi da ita sai sauran ayyuka su wayi gari wurgaggu.

    farin ciki ya tabbata ga wanda ya san iyakar kansa ya san shugaban shahidai (as) hakikanin sani, ya kuma gyara kansa da jama’arsa da yunkurin Imam Husaini (as) na kawo gyara, lallai shi ya fito ne domin kawo gyara cikin al’ummar kakansa kamar yanda ya fada amincin Allah ya tabbata a gareshi cikin wasiyyarsa ga `dan’uwansa Muhammad Ibn Hannafiya (kadai dai na fito domin kawo gyara cikin al’ummar kakana) wannan gayara na Husaini na kur’ani na Allah wajibi ne ya gudana cikin kowacce irin ibadar raya Ashura, wacce daga ciki akwai ziyararsa, musammam ma ziyarar Arba’in da miliyoyin al’umma ke zuwa daga sassan duniya, ya zama dole a kiyaye dokoki da ka’idojin addini cikin raya ta’aziyarsa da dukkanin abin da yake bayyanar da bakin ciki da damuwa kan shugaban shahidai da wadanda suka kasance tareda shi daga iyalansa da Sahabbansa amincin Allah da karamci ya tabbata a garesu haka daga cikin daurarrun iyalansa da yan’uwnasa da aka janyo a daddaure da sasari tun daga Karbala har zuwa Sham, a yau sanin wadannan ka’idoji da dokoki na kasancewa karkashin haskakawar Maraji’ai nagargaru da suka cika sharudda.

    Sannann daga cikin mafi muhimmancin abin da yake bukatar duba cikin ibadojin raya zaman makokinsa shi ne bakin ciki da nuna damuwa da kuka, babu banbanci cikin kasantuwarsa kan mimbarori ne ko ciyar da dukan kirji ko kuma ciyar da abinci ko dukkanin wata ibada, kai hatta cikin wakoki da kasidodji, alal misali idan sun kasance ana rera su da da sanannun shakalin wakoki da yanayin da zai ribaci mai sauraro zuwa garesu, to lallai akwai matsala, Allah ne mai katangewa.

    Sannan bai buya ba kamar yanda yake a tabbace da idanu da sani ballantana ma dalili da kur’ani, kamar yanda tarihin ta’aziyar Husaini yake shaidawa tun zamanin A’imma tsarkaka har zuwa zamanin da muke ciki wannan batu na Husaini (as) da ibadojinsa da suka d ace da shari’a masu albarka da ake samun lada kansu lallai suna daga jan layi duk wanda ya tsallaka zai fadi warwas ya kuma halaka ko da kuwa shi ne mafi sani da ilimi a zamaninsa, saboda ayi taka tsantsan ayi taka tsantsan daga taba wadannan ibadoji na ta’aziya da suka dace da shari’a, lallai su fa kamar garwashin wuta basa takuwa.

    Da sannu Husaini (as) da Ashura za su wanzu saman kowa da kowa tareda dukkanin bakin ciki da kiyayyar makiya, dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai.

    BAWAN ALLAH ADIL `DA GA ASSAYID ALI-ALAWI.

    HAUZA ILIMIYA