sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • MAULIDIN IMAM HASSAN ASKARI
 • SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI CIGABA DA BAHASUL KARIJ
 • MUNA MIKA TA’AZIYA GA DAUKACIN GURGUZUN AL’UMMAR MUSULMI BISA SHAHADAR IMAM ALIYU IBN MUSA ARRIDA (A.S)
 • TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH DA DANSA IMAM HASSAN (A.S
 • SABUWAR SHEKARAR MUSLUNCI 1441 TARE DA DAWOWA KARATU DAGA RANAR ASABAR 14 GA WATAN MUHARRAM
 • BAYANI DANGANE DA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAM SHEKARA TA 1441 H
 • BAYANI KAN MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAHAM SHEKARA 1441 H KASHI NA (2)
 • BAYANI NA FARKO (1) BISA MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAMAN SHEKARA 1441 H
 • TASHAR KARBALA IRFAN ZASU WATSA LACCOCIN ASHURA NA SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI
 • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Suldanul Nufus Aliyu bn Musa Arrida (as)
 • Makalar Hubbun Nisa’i fi Hadisun Nabawi ta fito- tare da Alkamalin Assayid Adil-Alawi
 • Makalar Annaji Bashar Mau’udul Muntazar ta fito tareda Alkalamin Assayid Adi
 • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Jafar bn Muhammad
 • Makalar duba li mushatulArba’in tareda Alkalamin Assayid Adil-Alaw
 • Allah ya girmama ladan ku da na mu bisa musibar rashin Sarkin muminai Ali (as)
 • Tunawa da Ranar haihuwar Imam Aliyu bn Husaini Zainul Abidin Amincin Allah ya tabbata a gare shi
 • Maulidin Abul Fadlul Abbas bn Ali (as) and akewa lakabi da Kamaru Banu Hashim mai shayar masu kishi a Karbala
 • Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Jawad (as)
 • Ranar asabar 14 ga watan Rabi’u Awwal Assayid Adil-Alawi (h) zai cigaba da bada darasin bahasul karij
 • muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar da aka haifi Imam Hassan Askari (as)
 • Labarun da ba tsammani

  Labarai wanda akafi karantawa

  BAYANI KAN MUNASABAR ZAGAYOWAR WATAN MUHARRAHAM SHEKARA 1441 H KASHI NA (2)

  Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

  Amincin Allah ya tabbata a gareku yaku muminai masoya Husaini (as)

  Bayan haka, hakika Allah ta’ala cikin littafinsa mai girma yace:

  ﴿وَمَنْ يُعَظِّمْ شَعَائِرَ اللَّهِ فَإِنَّهَا مِنْ تَقْوَى الْقُلُوبِ[1].

  Duk wanda ya girmama ibadojin Allah lallai tana daga takawar zukata.

  Mamaki ta kaka cikin jihadi da yakar yan ta’addan Salafiya (Da’ish) muna sadaukar da rayukan a zubar da jinanen mu karkashin fatawar Maraji’ai Salihai amma kuma cikin raya wasu ba’ari daga ta’aziyar Imam Husaini (as) sai mu dinga karbar fatawa daga Haura’u Zainab (as).

  Hakika Assayada Zainab (as) raina fansa gareta bata laminci hakan ba, lallai ita kamar Imam Zaman Alhujja (as) ce, tana mayar da mu zuwa ga Fakihai a zamanin gaiba Kubra, sannan shi Marja’i fakihi wand aya cika sharudda shine wanda yake komawa zuwa ga Assayada Zainab (as) domin karbar hukunci daga riwaya da tarihi da hadisanta, domin ya tantance rarrauna daga ingantacce da hadisan da suke da isnadi da ababen la’akarim domin ya tantance wuraren da akai kara da juna cikinsu, kuma ya hada tsakaninsu da hadawa da kafa hujja ko jam’il tabarru’i, tana iyab yiwuwa abinda aka rawaito daga gareta da sauran Ahlil-baiti ya kasance rarrauna cikin isnadi da dalala, ko kuma ya kasance yana cin karo ba zai iya yiwuwa a warware matsalarsa ba da jam’il dalala ko na tabarru’i sai ya zama ya tilasta faduwarsa, ko kuma ya kasance yana sabawa hankali ko wani abu makamancinsa, sakamakon abinda yake kewaye da shi daga matsaloli da ishkalai na fanni wadanda masana fannin tantance hadisai da riwaya daga fakihai su ke tsinkaye a kansu(Allah ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya daga cikinsu ya kuma kare wadanda suke rage)

  Abinda yafi kamata daga kowannce mawaki da mai rera wake dama duk wani mai karanta huduba da dukkanin wanda yake raya zaman makoki da ta’aziyyar da majalisan jimami da maukibai da dukkanin wani mas’uli kai har ga zuwa matashi balagagge wanda yake hidima cikin maukibi wajibi aikinsa ya kasance ingantacce karbabbe a hankalce da shari’a domin ya samu lada kan aikin ka da ya bige da janyo kansa azaba da ukuba, ka da kuma ya zamanto ya cutar da shugaban shahidai (as) da aikinsa, domin shugaban shahidai (as) kamar mahaifinsa Sarkin muminai (as) yake cikin fadinsa amincin Allah ya kara tabbata a gare shi :

   (قَصم ظهري إثنان: عالم متهتك لا يعمل بعلمه، وجاهل متنّسك يعمل بجهله ويعبد ربه عن جهل).

  Mutane biyu sun karya mini gadon bayana: da malami mai keta alfarma wanda baya aiki da iliminsa, sai kuma jahili mai ibada yana aiki da jahilci yana bautawa ubangijinsa kan jahilci.

  Duk wanda yake raya ta’aziyyar Husaini (as) kan jahilci da son rai, lallai shi babu shakka yana karya gadon bayan Imam Husaini (as) da kofaton kafafun dokin jahilcinsa. Yana karya gadon bayan wanzazzen yunkurin Imam yana kuma rusa gininsa na kawo gyara cikin al’umma da dukkanin mutane da aikinsa na jahilci da bata, lallai al’ummar muslunci sune mafi alherin al’ummomi da aka fito da su aka samar da su domin mutane, lallai Allah ya cika Annabta da manzanci da cikamakin Annnabawa shugaban manzanni Muhammad (s.a.w) ya aiko shi da shiriya zuwa doran kasa don tabbatar da adalci da daidaito bayan an cika kasa da zalunci da danniya.

  Sannan kamar yanda muke kira zuwa ga shi’a masu wilaya da masoya Husaini (as) da dukkanin bangarorinsu da banbance-banbance harshensu ya zuwa ga taimako kan raya zaman makokinsa da dukkaninh abinda Allah ya hore musu daga karfi da nishadi da dukkanin kamala, da dukkanin abinda yake bayyanar da bakin ciki da sanya kuka, haka zalika muna jan kunnenmsu muna yi musu gargadi daga ayyukan jahilci da wauta da shirirta da hauragiya da dukkanin abinda yake bakanta fuskar mazhaba.

  Lallai shi muslunci da Manzon Allah (s.a.w) kamar yanda ya kasance mai bushara a daidai wannan lokaci kuma ya kasance mai gargadi, ya kuma kasance fitila mai haskawa Manzo mai bada shaida, Allah shi ne masanin manufa.

  Godiya da yabawa ga jagororin ni’ima, farin ciki ya tabbata ga masoya Husaini cikin kukansu da shashshkarsu da sadaukarwarsu cikin raya ibadojin zaman juyayi halastattu da suke dacewa da hankali, lallai suna daga ibadojin Allah, duk wanda ya raya ibadar Allah lallai hakan na daga tsoran Allah.

  Daga cikin abin da ba boye yake daga dukkanin mumini da mumina shine cewa al’amarin shugaban shahidai (as) da ranar Ashura da kasar Karbala da ibadojin ta’aziyyar Husaini halastattu lallai suna daga tajallin hasken Husaini (as) da fitilarsa ta ubangiji (lallai Husaini fitilar shiriya ne kuma jirgin tsira) shi hasken Allah ne mafi girma da makiya da masu shakku kullum suke kokarin kawo shubuha da cikas kansa.

  Suna ta kai kawo don bushe hasken Allah matsarkaki sai dai kuma cewa Allah zai cika haskensa da yake tajalli cikin fansar jinin shugaban shahidai amincin Allah ya kara tabbata a gareshi ko da kuwa musrikai da kafirai basa so.

  Sha’a’irul husainiyya halastattu suna daga jan layi duk wanda ya kusance su ya nemi ketare su ya halaka ya lalace

  Farin ciki da aljanna su tabbata ga wanda yake gaggawa cikin raya su da kafafunsa da alkalaminsa da jininsa, lallai shi shugaban shahidai tafarki ne mikakke tareda wadanda Allah yayi ni’ima kansu daga Annabawa da Siddikai da Shahidai da Saliahi sun kyautata zama abokai, karshen maganarmu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai

   اللّهم عجّل لوليك الفرج والنصر والعافية

  Ya ka gaggauta bayyanar waliyinka  ka bashi lafiya.

  Ya Allah ka amsa ya ubangijin talikai  tsira da aminci suka tabbata ga Muhammad da iyalansa tsarkaka