lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

KARIJUL FIKHU 27 RABIU AWWAL 1441 H CIKIN TA'ARIFIN IJTIHADI A ISDILAHIN FIKHU TSAKANIN SUNNA DA SHI'A

Wuri: Qum Mukaddasa-cibiyar Jabalul Amil Islami tare da Ustaz Assayid Adil-Alawi

Lokaci: karfe 9 na safe, Usul 28.

Cigaba kan bahasin da ya gabata: cikin ta'arifin Ijtihadi a isdilahin fikhu daga bangarori biyu: hakika Muhakkikul Hilli yayi ishara ya zuwa ta'arifin guda biyu na farko shi ne ta'arin da Haji daga bangaren sunna na biyu shi ne ta'arifin Allama wanda ya kasance: (sadaukar da kokari cikin samo hukuncin shari'a).

Bai buya ba cewa abinda yake a cikin Alkawanin juz 2 sh 100 da aka nakalto daga Haji da Allama shi ne (fakihi ya sadaukar da karfinsa) haka ma cikin littafin Alma'alim sh 232 wannan kenan da fari, amma na biyu: cikin ta'arifin Allama akwai kari sai dai cewa Akaramakallahu bai kawo shi ba, lallai yand alamarin yake shne cikin littafin Nihayatul Wusul anyi ta'arifin Ijtihadi da (amma cikin duniyar Fakihai lallai ijtihadi na nufin saduakar da karfi cikin neman wani daga hukuncen-hukuncen shari'a ta yanda zargi zai kau daga gareshi da dalilin takaitawa).

Sannan ya ce: kadai dai munce cikin neman zato domin fitar yankakkun hukunce-hukunce daga cikinsa, a bisa kammalallen ta'arifi wanda ya tattaro dukkanin daidaikunsa ya kuma hana barai shiga cikinsa, kaidoji cikin kammalallen ta'arifi suna kasancewa kaidojin katangewa bawai na bayani ba.

Sannnan Allah ya tsarkake ruhinsa ya ce: fadinmu daga hukunce-hukuncen shari'a mun fadi hakane domin mu fitar da shi da al'amuran hankali.

Sannan fadinmu: ta yanda zargi zai kau da sababin takaitawa domin ijtihadin mai aksa a gwiwa da takaitawa ya fita tare da yiwuwa kari kansa, lallai ba a kirga shi daga ijtihadin ingantacce, sannan babban malaminmu Shaik Ansari Allah ya tsarkake sirrinsa ya ce: (yin ijtihadi koma bayansa ba abu mai yiwuwa ba).

Ijtihadi a gurin Allama bai nufin neman mudlakin zato kamar yanda yake a wurin Haji daga sunna, bari dai abin nufi daga gareshi kebantaccen zaton da ake la'akari da shi wanda babu Karin wani abu a kansa daga bincike.

Amma ta'arifi na biyu daga wasunsu ina nufi Haji da Allama kamar yanda aka hakaito daga Shaik Baha'i Allah ya tsarkake sirrinsa cikin littafin Zubdatul Usul sh 407 shi ne wata malakace da mutum yake samun iko karkashin inuwar ta ya ciro hukunci shari'a na reshe daga asalinsa a take da tanadi na kusa.

Wannan ta'rifi kadai an nakalto shi daga ma'anar lugga kamar dai ta'arifin farko daga kasancewa da Ammi zuwa Kassi shi yana daga sanannen nakali kamar yanda ya gabata, sannan dacewa tsakanin wannan ma'ana da ma'anar lugga ta kasance daga dangantaka ta sababi, hakika jurewa wahala da tsanani da sadaukar da karfi da iko kadai ya kasance sababin samun malaka, lallai ita bata da banbanci da kowacce malaka cikin kowanne irin fakihi kadai dai tana samun ta hanyar tamrini da tirenin da dukufa yau da gobe da yawan maimaici na ilimi da aiki.

Dogara da wannan ta'arifi ijtihadin isdilahi zai kasance daga malaka wacce ta kasance da kaifiya da siffar nafsu da take zurfafa cikin zuciya kamar misalin malakar tukin mota cikin direba, lallai direba duk sanda yah au mota zai tuka ta kai tsaye ko da kuwa ya bar tuki tsahon shekaru biyu, ka lura.

Sannan bayaninsu kan istinbadin hukuncin shari'a ko kuma neman samun zargi da zaton hukuncin shari'a harafin lamun da ya tare da ita ko dai ya kasance daga lamul istigraki sai ya zama yana nuni zuwa ga mudlakin ijtihadi ba tare da rarraba shi, ko kuma lamul jinsi sai ya tattaro daga mudlaki da mutajazzi.

Amma fadinsa: (daga asali) ma'ana yana nufin daga hujja da dalili kan mudlakin hukunci shin ya kasance daga Amaratul shar'iyya ne ko kuma daga Kbarul Sikatu ko kuma daga Usulul Amaliya kamar misalin bara'a da istishab.

Amma fadinsa: (na take ko kuma nan gaba kusa-kusa) dukkaninsu kaidi ne na isitinbadi, ai yana nufin: hakika shi istinbadi wani lokacin yana kasancewa nan take, kamar misalin ace da zai yi istinbadin hukunce-hukuncen shari'a da tsamo su daga cikin cikkunan dalilan na tafsili daga Kur’ani da sunna, wani lokacin yana kasance bisa dogara da tanadin nan gaba sai dia cewa kusa-kusa yake bawai nesa ba, ma’anar cewa lallai bai bugi kirji ga yin istinbadi sakamakon kebantaccen yanayi da yake da shi kamar misalin rasa daya daga sabubban istinbadi ko kuma sakamakon rashin hallarar dalili daga hadisai, (sabida wani abu da ya bijiro kamar misalin rashin lafiya ko safara tafiya da makamantansu) sai istinbadi ya kasance a wannan lokaci bisa tanadi na kusa-kusa kamar misalin haihuwar yaro daga mahaifiyarsa cikin karshen watan cikinsa lallai ya kasance mutum cikin maniyyi sai dai cewa cikin tanadi mai nisa, yayin kusantowar haihuwarsa sai ya kasance mutum cikin tanadi na kusa-kusa.

Ba da ban wannan kaidi ba da ya hana bare shigowa cikin ta’arifi da madaukaki da yake da yake da tanadin samun malakar tsamo hukunci ya zama mujtahidi tare da cewa shi ba mujtahidin bane, sai ijtihadi hukuncin ya zama irin daya da hukuncin likitanci, hakika yaro karami yana da tanadin zama likitan a zamani mai zuwa tare da hakan ba a kiransa da likita, amma wanda ya kasance cikin kwalejin koyan aikin likitanci kuma yana shekararsa ta karshe da za a yaye shi ya kammala karatun lallai shi ana kiransa da likita ko da kuwa majazan, ka lura.

Kaidi na karshe kadai yana shiryarwa zuwa abubuwa guda biyu: na farko: sanya ma’abocin malaka wanda baya istinbadi da tsamo hukunci nan take cikin ta’arifi

Na biyu: fitar da ba’ame shi ne wanda bai samu malaka a asali.

Mujtahidi a isdilahi: ko dia ya kasance wanda yake tsamo hukunci take ko kuma ya kasance mai tanadi kan haka tanadi na kusa-kusa a hankalce.

Sannan Akaramakallahu yayi ishara cikin mukamin neman uzuri daga tawaya da kosarwa cikin ta’arifofin kamar yanda ya kasance wurin magabata nagargaru da cewa ta’arifofin guda biyu da aka ambata basu kasance ta’arifofi ba cikakku da haddul tam jami’i mani’i da yake bayyanar abin da ake bukata a hakikance kamar yanda ake cewa: menene mutum idna ana son sanin zatin hakikarsa sai a kawo abinda yake nuni zuwa ga zatinsa daga jinsul karib da fasalul karibu kamar yanda yake a ilimin mandiki sai ace (haiwanul nadik) dabba mai Magana, shi ne hakikanin zati da zatinsa da hakikarsa, ta’arifin ijtihadi bai kasance daga irin wannan babin ba da har kaidojin shinge zasu kasance su kuma yaye sabanin malamai cikin hakikar ijtihadi da mahiyarsa da har nakadi da ishkali zai samu damar gangarowa kansa, ma’ana akwai wanda yake nakadi da kalubalantar ta’arifin ta fuskar ishkalul hukmi ko kuma iskalul ta’affi da cewa bai kasance cikakke da ya tattaro daidaikunsa ya kuma hana bare shigowa, bari dai kadai abin nufi daga misalin wannan ta’arifi shi ne daga babin sharhul ismi da ishara ya zuwa abinda ya kasance sananne a wurin wanda ake Magana da shi ya san shi a dunkule tun kafin yi masa bayani sai dai cewa ya san shi da wani sunan daban.    

 

Tura tambaya