lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

tsari daga sharrin Iblis

 

Salamu Alaikum Sayyid

Ni budurwace inada kimanin shekaru 18 Alhamdulillah na kasance bana sakaci da salla tun tasowa tun ina karama, sai dai cewa yanzu tsawon wani lokaci ban san me yake faruwa da ni ba shin kasala ce da gafala da nauyin cikin kaina, lallai hakan yana tasiri cikin karatuna dalili shine ina jin kunci cikin zuciyata  da dimauta da wasu tunane-tunane, ni ina jin cewa wannan abubuwa suna son nesanta ni daga addini na ni kuma bana kaunar faruwan hakan ta yanda na kai ga ina fatan cewa ina ma dai ni na riga na mutu na bar wannan duniyar, ina jin wani wasiwasi cikin raina da yake ce mini lallai zaki sha azaba, gaskiya nifa na gaji, wai me yasa haka yake faruwa dani, alhalin ni koada yaushe ni rike kam da salla da azumi da karatun kur’ani da addu’a, bawai ni kadai ba Alhamdulillah dukkanin yan gidanmu sune riko da addini in banda kanwata yar karama ita kadai ce bata salla munyi bakin kokarinmu wajen ganin tana salla amma hakarmu ta gaza cimma ruwa.

Ban san me yasa ba shin zaka fahimtar dani dalilin hakan ma’ana wadannan tunane-tunane da suke kaikawo cikin raina?

Lallai ni ina jin sun fara fin karfina, ina fatan ka sanya cikin addu’a Allah ya yaye mini wannan musiba.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Wannan yana daga aikin shaidanu daga aljanu da mutane, lallai shi Iblis bai kaunar kwanciyar hankalin mumini da mumina, zaka same shi yana takura musu.

Sannan kuma ki sani ita duniya gida ne jarrabawa da gwaj, ki sani abin da yake faruwa dake dole kiyi hakuri kansa ki kuma nemi taimako daga wurin Allah madaukaki ki dogara da shi (ku nemi taimako da da hakuri da salla) kad aki debe tsammani daga rahamar Allah da ni’imarsa lallai shine mafi jin kan masu jin kai shine kuma mai bad akariya ga bawansa daga sharrin ashararai daga Iblis da rundunarsa da mutanensa.

Allah ne abin neman taimako.

Tura tambaya