lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Kyawawan halayen likita ne a muslunci

Addu'a ita ce kur'ani mai tashi zuwa sama, hakika manzo mafi karamci Muhammad (s.a.w) da A'immatu Ahlil-baiti (a.s) sun himmatu da addu'o'i himmatuwa matuka, saboda ita addu'a ita ce mai warkar da zukata ita magani ce ga ciwuka, ita ce mai tsaftace zukata kuma makullin amsawar ubangiji da biyan bukatu, hakika A'immatu Ahlil-baiti sun bar mana dukiya mai tsadar gaske da tsarki daga addu'o'i masu tsaftace ruhi cikin fannoni mabanbanta daga addu'o'i da wuridai da Azkaru.

An ambaci cewa Sayyid ibn Dawus babban malamin da babu kamarsa a zamaninsa wanda dakin karatunsa ya kasance ya cika da litattafai da mujalladan addu'a kusan dari takwas wanda ya rawaito daga A'imma tsarkaka.

Wannan yana nuni kan girmamar addu'a da tasirinta mai isarwa cikin rayuwar mutum, lallai hakan yana kawo wanyewa lafiya da rashin zamewa daga kan shiriya da kauracewa duniya da komawa ga Allah da tanadi don lahira, da neman Allah ya yiwa bawa mu'amala da ludufinsa da karamcinsa da abin da yake ahalinsa, da samun azurta cikin gida biyu da haske da shiriya da sanin Allah da kaiwa zuwa ga kamala mudlaka da mudlakar kamala, da narkewa cikin zatin Allah matsarkaki madaukaki.

Bai buya ba a wurin ma'abota hankula cewa addu'ar da take samun amsuwa tana da sharudda wadanda malaman wannan fanni suka ambata, kamar yanda ya zo cikin littafin (Jami'ul Sa'adat) na Allah ya jikan rai Annaraki, da littafin (Mahajjatul Baida'u) na malam Faizul Kashani, da (Uddatu Da'i) na ibn Fahad Hulli da sauran litattafan Sayyid ibn Dawus, da littafin (Mafatihul Jinan) na Shaik Abbas Qummi, da gomomin litattafai da suka kan addu'o'i da Azkaru da wuridai.

Daga cikin mafi muhimmancin sharuddan: shi ne cikakken sanin Allah, da kuma aiki da abin da yake hukuntawa, da hallaro da zuciya da tausasata da jin kanta, da tsarkake kasuwancinka da neman halas, da biyayya ga Allah da manzonsa da A'imma tsatsonsa, da iklasi da tak'wa da yakini kan cewa Allah zai amsa, Imam Sadik (as) yana cewa:

«إذا اقشعرّ جلدک ودمعت عيناک ووجل قلبک ، فدونک دونک فقد قصد قصدک

Idan fatarka ta kwansare ta yankwane idaniyarka ta kwararar da hawaye zuciyarka ta razana, ka karba ka karba hakika ka cimma abinda kake buri.

 da tsarkake badini da fuskantar Allah matsarkaki da ikirari da zunuban da ka aikata da kyautata zato da Allah matsarkaki.

 

Tura tambaya