lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Malamai sune magada Annabawa

 

Dukkanin godiya ta tabbata ga wanda ya sanar ta hanyar alkalami ya sanar da mutum abin da bai sani ba, tsira da aminci su kara tabbata kan Annabawa da manzanni da jagororin shiriya wadanda suke isar da sakon Allah haka ma kan cikamakin Annabawa da Manzanni Muhammad da iyalansa malamai rabautattu A’imma tsarkaka.

عن الامام الصادق عن ابائه (عليهم السلام) قال : قال رسول الله (صلى الله عليه واله) : من سلك طريقا يطلب فيه علما سلك الله به طريقا الى الجنة وان الملائكة لتضع اجنحتها لطالب العلم ورضى به وانه يستغفر لطالب العلم من في السماء ومن في الارض حتى الحوت في البحر وفضل وفضل العالم على العابد كفضل القمر على سائر النجوم ليلة البدر وان العلماء ورثة الانبياء.

ان الانبياء لم يورثوا دينارا ولا درهما ولكن ورثوا العلم فمن اخذ منه اخذ بحظ وافر .

An karbo daga Imam Sadik daga babanninsa (a.s) yace: manzon Allah (s.a.w) yace: duk wanda ya bi wata hanya yana mai neman ilimi Allah zai dora shi kan hanya zuwa aljanna, hakika Mala’iku suna shimfida fukafukansu ga dalibin ilimi Allah kuma ya yarda da shi, lallai yanda al’amarin yake shine wadanda suke sama da kasa kai hatta kifi cikin ruwa suna nemawa masa gafara, sannan fifikon malami kan mai bauta kamar fifikon da wata ke da shi kan sauran taurari a daren cikar watan hakika malamai sune magada Annabawa.

Hakika annabawa basu gadar da dinare ko dirhami ba sai dai cewa sun gadar ilimi dukkanin wanda diba daga gareshi ya debi cikakken rabo.

Manufa daga wannan hadisi madaukaki shine mu maida hankali kan layin da ya zo a karshe wato (malamai magada Annbawa ne) hakika kalamin Imam kalami ne wanda cikinsa akwai haske da tarsashin haske mai kyalkyala da yake dauke da madaukakan ma’anoni kamar misalin Kur’ani  mai girma domin cewa ai su Imamai (a.s) sune nauyi na biyu daga nauyaya guda biyu  kuma sune tsaraikun Kur’ani mai girma da manzon Allah (s.a.) ya bar mana, musammam ma shi wannan hadisi daga gareshi aka ji.

Bai buya ba cewa lallai wannan gado gadar Annabawa tana da sasanni mabanbanta da janibobi masu tarin yawa da zamu Ambato ba’arinsu cikin takaitawa da yin ishara domin su kasance jagaban shaidu da alamomi ga wanda ya nufi tafiya mai zurfi cikin hanyar wannan hadisi madaukaki, saman dukkanin wani masani akwai mafi sani daga gare shi.

Daga cikin sasannin gado akwai:

1-gado na dukiya: malamai basa gadon Annabawa cikin dukiyarsu, kadai dai wanda yake gadon Annabi cikin dukiyarsa shine wanda ya kasance daga danginsa tsatsonsa, zasu gaje shi kan littafin Allah kamar yanda Sulaimanu (as) ya gaji Dauda (as) haka Yusuf (as) ya gaji Yakub (as), shi malami baya gadar Annabi cikin dukiyarsa da tarkacen sa na duniya dogaro da nassin fadinsa (s.a.w) (hakika su Annabwa basu gadarwa malamai dinare da dirhami ba) a wata riwayar kuma basu gadar da ruwan dorawa da fara ba ma’ana zinare da dirhami.

2- gado na ilimi: lallai malamai suna gadar Annabawa cikin ilimummukansu kamar yanda ya zo cikin nassi (sai dai cewa sun gadar musu ilimi) abin nufi daga ilimi anan shi ne ilimi mai amfanarwa wanda yake amfanar da wanda ya san shi yake kuma cutar da wanda bai san shi ba, ma’ana ilimin addini cikin Asalansa da rassansa (ilimin Fikihu da ilimin sanin Akida da ilimin Akhlak) kamar yanda hakan ya zo cikin riwayoyi madaukaka kamar yanda yake a fadin Annabi (s.a.w) kadai dai ilimi kashi uku ne aya bayyananniya da sunna tsayayya da farilla Adala.

3- gado na kyawawan halaye: hakika malami yana gadar Annabi cikin halayensa madaukaka da sulukinsa mai girma daga tawali’u da son talaka da kyautata dabi’a da hakuri da juriya kan musibu da wahalhalu da daurewa matsaloli saboda isar da sakon Allah, Annabi (s.a.w) shi ya kasance baki dayan dabi’unsa Kur’ani ne lallai shi yana kan halaye masu girma.    

Ilimi na Annabi ya zama tilas ya siffantu kyawawan halaye da karramammun siffofi domin an gado shi daga kyawawan halayensa (s.a.w) ita Magana idan ta fito daga kyakkyawar zuciya ta mai tsoran Allah mai kyawawan halaye sai ta shiga zukata, amma idan ta fito daga iya fatar harshe lallai bata ketare ko ina face fatun kunnuwa, ya zama wajibi ilimi ya jikkantu da haske da tajallin wilaya a zahirin sa da badinin sa.

4- gado cikin shiriyarwa da isar da sakon Allah: da kuma sanar da mutane da gargadin su da yi musu bushara da kiransu zuwa ga bautar Allah da tsarkake niyyya cikin aiki da tsorata su daga ranar alkiyama kamar yanda Annabawa suka yi cikin al’ummomin su

وجعلنا ائمة الحق يهدون بامرنا ) ( وارسلنا اليهم رسولا من انفسهم يتلو عليهم اياته ويزكيهم ويعلمهم الكتاب والحكمة ) ( انما عليك البلاع ) ( الذين يبلغون رسالات الله ) ( فلولا نفر من كل فرقة طائفة ليتفقهوا في الدين وليتذروا قومهم اذا رجعوا اليهم لعلهم يحذرون ) .

Muka sanya jagororin gaskiya da suke shiriya da umarnin mu. Muka aiko zuwa gare su manzo daga cikinsu yana karanta musu ayoyin sa yana tsarkake su yana sanar da su littafi da hikima.

Ba don wasu sun rage daga kowacce kungiya daga garesu domin su nemi fahimta cikin addini domin su gargadi mutanen su idan sun komo garesu tsammanin su sa tsorata.

Annabi ya kasance likita kuma magani yana magance cututtukan mutane da littafin Allah mai girma

 (وننزل من القران ما هو شفاء ورحمة ) (هدى للناس ) ( هدى للمتقين )

Muna sassaukarwa daga Kur’ani abin da yake waraka da rahama.

Shiriya ga mutane. Shiriya ga masu tsoran Allah.

Malamai da Hauzozin ilimi bai kamace su ba ace sun takaita kansu iya koyar da Fikihu ba domin hakan kamar koyar da likitanci ne sannan shi fa mai koyarwa ba shine likita ba.

Malami fakihi shi ne wanda yake koyar da Fikihu da bijirar da kansa fagen fama domin tarbiyantar da mutane da shiriyar da su da tsarkake su ya kuma lazimci isar da sakon Allah kamar yanda yake a bayyane hakan na tareda jurewa wahala da musibu daga dukkanin bangarorin zamantakewa, sai ya zama mai magance matsalolin mutane da abin da yafi kyawu

( امرت بمداراة الناس )

An umarce ni da kyawunta zamantakewa da mutane.

Hakika Annabawa sun kasance ana yanka jikin su da zarto (hacksaw) a janye shimfida daga karkashin kafafun jagorori, sannan kowanne Annabi yana da Fir’aunan zamanin sa, lallai muatne suna gaba da abin da basu sani ba, ya zama wajibi kan malami ya kiyaye abubuwan da suke damun mutane ya warware musu tareda dukkanin nuna kauna da Iklasi, lallai shi likita ne mai kekkewayawa da yake warkar da jama’a kowanne gwargwadon halin da yake ciki da ciwon sa mutane suna da wani yanauyyuka tareda jahilci  daga cikinsu akwai wadanda:

 (اذا خاطبهم الجاهلون قالوا سلاما )

Idan jahilai sukai musu Magana sai su ce aminci.

 Daga cikinsu:

 ( خذ العفو وامر بالمعروف واعرض عن الجاهلين )

Ka riki afuwa kayi umarni da sananne ka kauracewa jahilai.

Daga cikin su:

 (ولا تتبع اهوائهم من بعد ما جائك من العلم )

Ka da ka biyewa son rayukan su bayan abin da ya zo maka daga ilimi.

Daga cikin su:

 ( واصبر على ما يقولون واهجرهم هجرا جميلا ).

Ka yi hakuri kana bin da suke fadi ka kaurace musu kyakkyawan kauracewa.

5-gado cikin zaba: lallai Allah yana zabar Annabawa da manzanni tsakanin halittun sa

 ( واصطفى ربك ادم )

Ubangijinka ya zabi Adamu.

Ya kuma kiyaye su daga zunubai da aikata laifuka da mantuwa da rafkana da isma ta zati, haka zalika yana iya zabar malamai daga halittun sa, sai dai cewa wajibi kansu su katangu da Katanga da ismar aiki su daukaka kawukansu daga aikata zunubai da laifuka da ayyukan makaruhi, idan ko ba haka zau jarrabtu da ukubar Allah mafi kankanta daga gareta shi ne ya cire musu jin dadin ganawa da shi kamar yanda hakan ya zo cikin madaukakan riwayoyi.

6-gado cikin albarka: lallai  Annabi albarkantacce ne cikin rayuwarsa ta daidaita da kuma tareda mutane shi mabayyanar albarkar Allah ne kamar yanda Ruhullah Isa Bn Maryam (as) ya fadi:

 ( وجعلني مباركا )

ya sanya ni albarkantacce.

Annabawa sune mabubbugar albarkoki ita albarka alheri ne mai tarin yawa madawwami tabbatacce kamar yanda yake a luggance, shi kuma malami magajin Annabawa ne cikin albarkarsu, su albarkantacce ne cikin rayuwarsa da alkalaminsa da kafarsa da bayaninsa da fuskarsa domin shi kamar misalin kyandir ne (candle) yana kone kansa haskaka mutane, ya zama wajibi malami ya kasance mabubbugar alherai da albarkoki cikin assasawa da gudanar da ayyukan addini da sakafa da taimakon jama’a kamar misalin gina makarantu da asibitoci cikin gari da masallatai da husainiyoyi da yada ilimummuka na gaskiya da dukkanin shakalansu da makamantan haka.

 7-gado na jihadi: lallai kowanne Annabi yana da makiyi, lallai Allah ya aiko Annabi domin shiriyar da mutane da tsayar da adalci sannan kuma ya umarce shi da yakar dawagitai  tun farkon da’awarsa har karshen numfashinsa, zargin mai zargi bai damunsa kan sha’anin Allah, kuma kiyayya masu girman kai ba ta dakushe himmarsa, haka lamarin yake kan malami lallai shi wani yanki daga yankin shiriyar da mutane zuwa hanya madaidaiciya da yakar dawagitai da jabberai da dukkanin mai yunkurin bautar da mutane da cin gallarsu da shagaltar da su daga barin bautar Allah da neman kusanci zuwa gare shi, hakika Allah ya fifita mujahidai kan mazauna da lada mai girma. Malamai kamar Annabawa suna yakar makiyan Allah makiyan addinin sa.

8- gado cikin nauyin ukuba: hakika Annabi sakamakon barin abin da ya kamata da yayi ya fita daga aljanna  kamar misalin Adamu (as) Annabta ta fita daga tsatsonsa kamar yanda ta faru da Yusuf (as) yayi kuka da raraji tsawon rayuwarsa har ta kai ga an kira da shi da Nuhu, to haka zalika malamai lallai yanda lamarin yake ana gafartawa jahilai zunubi saba’in gabanin gafartawa malami zunubi daya, idan har ya zamanto kyakkyawan aikin rabautattu mummanan makusanta ce kamar yanda ya zo a riwaya, to haka zalika kyawawan aikin jahilai munanan aiki ne ga malamai, mafi kankantar abin da za a yi wa malami mai aikata zunubi shine raba shi da jin dadin ganawa da Allah, malami nawa ne aka cire masa ni’imar ilimi sai ya wayi gari ya fita daga zirin malamai yayin da ya zamanto bay a aiki da iliminsa ya kuma wofinta da nauyin da yake kansa daga shiriyar da mutane da nusantar da su.

Ya zo cikin maduakakin hadisi cewa malamin da bay a aiki da iliminsa yake kuma sabawa ubangijinsa yana jarrabtuwa da dayan uku: ko dai mutuwa yana saurayi, ko zama hadimin sarki kamar misalin malaman fada, ko kuma ya kasance cikin fili gona.    

9-gado cikin hukuma: Annabta shugabanci ne cikin harkokin addini da duniya da nassi daga Allah matsarkaki, Annabi shine jagoran mutane cikin addinin su da duniyar su, lallai addini tsari ne kuma daula ne ya zo cikin madaukakin hadisi cewa malamai sune jagorori, sune magada Annabawa cikin shugabancin su ga jama’a zuwa alherai da kawo gyar, lallai da sannu bayin Allah nagargaru zasu gaje kasa kamar yanda nassin Kur’ani yayi bayanin hakan lallai kuma galaba tana ga Allah da manzanninsa:

 ( لاغلبن انا ورسلي )

Tabbas ni da manzannina za mu yi galaba.

Malamai sume masu jin tsoran Allah

 ( انما يخشى الله من عباده العلماء )

Kadai masu jin tsoran Allah daga bayinsa sune malamai.

Ilimi yana kira zuwa ga gyaruwa da kawo gyara kamar yanda shi gyara dama yana tareda ilimi, bayin Allah salihai wadamda za su gaji kasa sune malamai nagargaru mafi alheri, lallai su ne jagorori masu shiriyarwa kuma hannunsu ragama al’amura yake sune zasu riki madafin iko karkashin sanya idanuwansu tafiyar da hukuma zai kasance sune magada Annabawa.

 10- gado cikin dabakoki: Shaik Saduk (r) cikin littafinsa Attauhid yana cewa: hakika annabawa daba-dabake ne hawa-hawa ne a cikinsu akwai wanda yake an aiko shi ga iya kansa akwai kuma wanda iya danginsa akwai wanda iya yankinsa akwai kuma na iya kasarsa, akwai kuma Annabawam da aka aiko su ga baki dayan duniya sune Ulul Azmi ma’abota litattafai na duniya baki daya a zamaninsu har zuw akan cikamakin Annabwa da manzanni Muhammad shi sakonsa ya kasance ga baki dayan mutane lallai shi rahama ne ga dukkanin halittu, kuma halal dinsa halal ce har zuwa tashin Alkiyama haka ma haram dinsa haram ce har tashin alkiyama.

Malamai magada Annabawa daga cikinsu akwai wanda ake kasancewa cikin mukamin tseratar da kansa da wasunsa.  

 ( قوا انفسكم واهليكم نارا)

Ku ceci kawukanku da iyalanku daga wuta.

Da kuma jagorantar siyasar mahallinsa da kuma kasancewa limami a masallaci da warware matsalolin mutane da rayuwa cikinsu da tseratar da kasa zuwa gabar azurta da alheri, ta iya yiwuwa sakonsa ta kasance ta dukkanin duniya ta kuma kasance baki dayan duniya ta amfana da ita da ilimin da ke tattare da ita mai albarka, kamar misalin maraji’an taklidi Allah ya saka musu da alheri, kadai Allah ya na wurga ilimi cikin zuciyar wanda yake so, su zukata kwaryoyi mafi alherinsu it ace mafi kiyayewarsu, wajibi kan dukkanin duniyar musulmi suyi duba mafi nisan duba cikin mutane su fadada tunaninsu da azamarsu da nishadinsu da siyasarsu  sun shiri da tsari ga kowacce al’umma su himmatu al’amuran musulmi lallai duk wand aya wayi gari bai damu da al’amuran musulmi shi ba musulmi bane yaya kuma ga malamai wadanda su ne jagorori makiyayaز

Wannan Kenan sannan daga cikin alfahari ga malamanmu shi ne kasancewa sune suka gaji Annabawa har ya zamanto cikin hakkinsu an ce:

 ( علماء امتي كانبياء بني اسرائيل )

Malaman cikin al’ummata kamar misalin Annabawan Banu Isra’il ne.

 A wata riwayar kuma

 ( افضل من انبياء بني اسرائيل )

Sun fi daraja daga Annabwan cikin Banu Isra’il.

Wannan wani takaitaccen bayani ne ga wasu ba’arin sasannin gadon Annabawa sannan akwai gomomin sasanni kamar yanda cikin kowanne sashe guda daruruwan sasanni suke reshentuwa. Ba a baku komai daga ilimi ba face kankani

Tura tambaya