lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Falsafa da siyasa cikin muslunci

 

Muslunci addini ne dacacce mai tattaro komai mai sabuntuwa ya tattaro dukkanin hukunce-hukunce da dokoki na lazimi da larura domin kamalar mutum babu banbanci cikin kasantuwar kamalar a matakin daidaiku ko jama'a, kamar yadda lallai gabatar da kebantaciyyar warwara ga batutuwan siyasa wadanda suke fuskantar mutane ana kirga su wasu yanki na asasi muhimmi hakama daga sakon addini, daga nan da farko yake zama tilas kan mu bijiro mai kewaya mai gamewa da mas'aloli mafi mhummanci cikin wannan fage domin samun amsar da shugabanni ga batutuwan siyasa suke bukatuwa zuwa gare su.

Bisa bijiro da su ga bahasosin asasi cikin system din siyasar muslunci, falsafar siyasa tana gabatar mana sura mabayyaniyar alamomi daga shakalin hukumar muslunci, kari kan haka tana ishara zuwa ga fifikon addinin muslunci a kebantacce da kuma addinan sama bisa shakalin gamewa saboda aunawa da makarantun tunani na mutum cikin fagen siyasa hakan ya kasance karkashin kalubalenta ga sauran tsarurrukan siyasa na zamani.

Hakika an tanadi wannan littafi da talifinsa don wannan manufa da hadafi cikin kokarin samar da bayani da tafsiri ga na hankali kebantacce ga bahasosi masu fadin gaske kuma asasi cikin tsarin siyasar muslunci, saboda haka mafi muhimmanci bahasosi wadanda wannan yanki wannan juzu'i daga wannan littafi zai mai da hankali kai wadanda suke da alaka da tsarin siyasa a muslunci sune:

Karin bayani ga mafhumai masu dangantaka da bahasin;

Larurar kafa hukumar muslunci;

Alaka tsakanin addini da siyasa;

Tabbatar da Alaka tsakanin addini da siyasa;

Hakikanin hukumar muslunci;

Bayani kan me cece hukumar muslunci da bayanin kan larurar samar da ita;

Tushen shari'a;

Tabbatar da shari'a da hukuncin wadanda sukai imani da Allah;

Tabbatar da cancantar wilayar annabawa da imamai ma'asumai da hukumarsu;

Rinin addini ga hukumar annabawa da imamai ma'asumai;

Ma'anar wilayatul fakihi da mafi muhimmanci bahasosi da suka ratayu da ita.

Tura tambaya