فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ GABATARWA
■ FASALI NA 1
■ WANE NE MAI TARBIYA ?
■ KASHE-KASHEN TARBIYA
■ ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA
■ IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI
■ IYALI A LUGGANCE
■ FASALI NA 2
■ AUREN DABI'A
■ AUREN SHARI'A
■ KASHE-KASHEN AURE
■ ADADIN MAZAJE
■ HANYOYIN TABBATAR AURE
■ kasantuwan miji daya rak mace daya rak
■ FASALI NA 3
■ DALILAN DAKE SANYA YIN AURE DA MANUFOFINSA
■ SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE
■ DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA
■ TAUHIDI
■ TAKAWA
■ MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH
■ SUNNAR ANNABI
■ KARUWAR ARZIKI
■ KARUWAR IMANI
■ ALFAHARI
■ KARUWAR IBADA
■ GARKUWA
■ SADAR DA ZUMUNCI
■ RIKO DA ADDINI
■ DEBE HASO
■ FASALI NA 4
■ DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE
■ ASALI
■ WATA CIKIN BURUJIN AKRABU
■ HUKUNCIN ILIMIN BUGA KASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
■ MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI
■ SON MATA
■ MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA
■ 1MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI KARANCI SADAKI
■ KARANCIN BUKATU DA SAUKAKE HAIHUWA
■ KASHE-KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU
■ TSARA CIKIN AURE
■ FASALI NA 5
■ YARDA SHARADI NE CIKIN AURE
■ FAFUTIKA CIKIN AURE
■ AUREN WURI
■ HUDUBA
■ SADAKI
■ HATSARIN TSADAR SADAKI
■ AUREN SHARI'A
■ DAREN ANGONCI
■ KABBARA
■ AYYUKAN DAREN ANGONCI
■ ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI
■ WALIMA
■ RARRABA ALEWA KO DABINO
■ LADUBBAN SADUWA DA IYALI
■ MAFI DADIN DADADA
■ WASA DA MATA GABANIN JIMA'I
■ LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA NA MAKARUHI
■ HUKUNCIN AZALO
■ ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI
■ FASALI NA 6
■ HAKKOKIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI
■ HAKURI
■ KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA
■ HAKKOKIN MACE
■ CIYARWA DA YALWATAWA
■ TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI
■ KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA
■ UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA
■ GARKUWA
■ KYAUTATAWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ KYAWUNTA ZAMANTAKEWA
■ HAKKOKIN MIJI
■ NEMAN IZINI CIKIN AIKI DA TASARRUFI
■ TAUSAYAWA MIJI
■ HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYAYYAKINSA
■ HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAKKOKI
■ JIMA'I
■ ADO
■ KAMEWA CIKIN MAGANA
■ MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA
■ SHUGABANTAR IYALI
■ DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE
■ SON JUNA
■ YAWAITA AIKATA ALHERI
■ SANYA FARIN CIKI
■ BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI
■ KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA
■ TAIMAKO DA TALLAFAWA
■ TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA
■ KALAMIN AKIDOJI MAI KYAWU DA KARFAFAFFEN FURUCI
■ KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI
■ BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI
■ KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI
■ RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI
■ RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE
■ RASHIN GORI KAN MIJI
■ RASHIN KAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA
■ YIN SHAWARA DA MATA AMMA BANDA BIYE MUSU
■ TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA
■ HANKALTA
■ MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA
■ KISHI
■ TAIMAKEKENIYYA
■ DADADAWA IYALI
■ TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.
■ BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA
■ KYAWUNTA ZAMA DA MIJI
■ WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE
■ HIDIMA MADAWWAMIYA
■ GODIYA
■ KAUNAR JUNA
■ TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA
■ FASALI NA 7
■ MUKAMI NA FARKO
■ SON `YA`YA DA KANAN YARA
■ MUKAMI NA 2
■ DA NAMIJI KO MACE
■ MUKAMI NA 3
■ NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI
■ MUKAMI NA 4
■ RAINON CIKI DA LADUBBNSA
■ MUKAMI NA 5
■ TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I
■ MUKAMI NA 6
■ HAIHUWA
■ MUKAMI NA 7
■ SHAYARWA
■ MUKAMI NA 8
■ RADIN SUNA
■ MUKAMI NA 9
■ TAYA MURNA DA SAMUN `DA
■ MUKAMI NA 10
■ AKIKA
■ WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN
■ MUKAMI NA 11
■ KACIYA
■ MUKAMI NA 12
■ KAMANCECENIYARSA DA MAHAIFINSA
■ MUKAMI NA 13
■ MATAKAN TARBIYYYAR YARA
■ MUKAMI NA 14
■ ADALCI TSAKANIN `YA`YA
■ MUKAMI NA 15
■ SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO
■ FASALI NA 8
■ HUKUNCE HUKUCEN MATA DA YARA
■ FASALI NA 9
■ BATUTUWA DABAN-DABAN
■ FASALI 10
■ SAKI
■ GABATARWA
■ HAKIKANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI
■ WAYE ME LADABTARWA
■ ME NENE LADABI
■ ASALAN LADUBBA
■ MASADIR CIKIN LADUBBA
■ MASADIR DIN LARABCI
■ SUNAN LITTTAFI DA SUNAN MARUBUCINSA

MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA

 

mutum a dabi'ance yana karkata ya zuwa kyawu da abu mai kyawu  hakika son kyawu da kyakkayawan abu ne wanda yake daga halittar dan adama da bai iya guje masa, shi yasa cikin komai yana kokarin ya ga ya samu mafi darajarsa da kyawu  sau da yawa ya kanyi kuskure cikin fahimta da gane abu mai kyawu, cikin kissar aure yana bincikar mafi darajar mace,  muslunci ya yi ishara da hakan bai gafala da wannan bangaren ba a cikin rayuwar mutum, sai ya yi bayanin mata masu mutunci, hakan na nufi da cewa mata su yi ado da irin wadannan darajoji  don su sami shiga cikin wadannan da aka siffantasu da mata masu daraja su kasance cikin masu albarka,

Cikin wadannan darajoji akwai wanda a zatinsu suke akwai kuma wadanda nemansu su ake da tsiwirwirarsu, dayawan  wadanda ake tsiwirwira sun canja sun koma kamar zati sun cike faraga da nakasar  da take tare da su, hakan yana ishara da cewa mata su zage dantse wajen neman falala da darajojin kyawawan dabi'u da al'amurran badini. 

Muslunci na jebantar bangaren kyakkayawar dabi'a wajen zaben miji tsoron Allah da imani sune tushen ma'auni sabanin kudi da dukiya da kyawu, wanda ya ke kallon abubuwan zahiri cikin aure daga dukiya da alfarma da kyawu kadai,to yana tafka kuskure a mahangar muslunci, saboda dukkanin wadannan abubuwa masu gushewa ne, kadai abun da ke wanzuwa shi ne kyawawan dabi'u da imani mai zurfi da tsoron Allah da kame kai da tsarki da siffofi tsarkaka wadanda suke mazharin sunayen Allah kyawawa da siffofinsa wanda suke wanzazzu da wanzuwarsa madawwami,  sune turaku tabbatu da guguwa bata iya girgizasu, basa girgiza tare da dukkanin jujjuyawar zamani, aure na daga yankin abokantaka da aminintaka, abokai kuma sashensu ga sashen makiyane face masu tsoron Allah. abokantaka daga ta aure wadda ta ginu kan tushen takawa tun ranar farko ita tafi cancanta da wanzuwa, sannan ta cigaba duniya da lahira, ta wayi gari mafi kyawu daga matan aljanna cikin dausayin aljanna, gangar jiki na karewa ruhi kuwa yana wanzuwa har sai jiki ya kara dowowa gare shi ranar alkiyama don ya kammala mutum  karo na biyu. mace da namiji albarkacin abin da suke dauke da shi daga imani da aiki nagari da kyawawan dabi'u , saboda haka mata sai su dage da neman kyawawan dabi'u da darajoji.

Ba zai yiwu a wadatu da barin aure ba domin shi aure hanya ce ta sunnar rayuwar wadda ke kare wanzuwar nau'in mutum da abubuwan da ke biye  da shi na daga tsarin zamantakewa da dabi'ar halittar mutum da sha'awarsa  wadda bai iya gafala daga barinta da watsi da kosar da sha'awarsa ta jinsi wacce bazai taba iya kangeta ba domin yin hakan na iya kawo gurbata da karkacewa ya zuwa munana ayyuka da rushewar al'ummada afkawa fushin ubangiji. kamar yadda a irin wannan lokuta ake jarrabar mutum da cutukan zuciya da kwakwalwa da ganganr jiki haka dangantaka ta halaka  ta kare da dai makamancin wannan.

Saboda haka bukatuwar mutum ya zuwa ga aure bukata ce ta dabi'ar halittarsa da bai iya guje mata, ta hanyar aure ne mutum ke kammala ya hau matakai ya kai ga darajoji  ya filfila cikin sararin samaniyar karamomi ya rabauta da arzikin gida biyu.

Ku taho muje birnin falala da darajoji wadanda muslunci ya shimfida mana, maza da mata ku taho ya zuwa kyawawan dabi'u, ya zama wajibi ga `ya`ya mata su tsiwirwiri falaloli da daraja, su canja da sauya abin da ke tattare da su daga munanan dabi'u zuwa kyawawa, hakika mata  sun karkasu kashi kashi kamar yadda maza suka kasance, riwaya na ishara da hakan a bayyane ga kadan daga misalin mataye salihai nagargaru.